BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa sun ƙi amincewa da shugabancin Matawalle a APC ta Zamfara

 119158626 Matawalleyari.png Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da tsohon gwamnan jihan

Thu, 1 Jul 2021 Source: BBC

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da tsohon dan majalisar dattawa Kabiru Marafa sun yi fatali da rahotannin da ke cewa Gwamna Mohammed Bello Matawalle ne jagoran jam'iyyar APC a jihar.

Sun bayyana haka ne a hirarsu da BBC Hausa jim kadan bayan sun gana da Gwamna Nasir Elrufai na jihar Kaduna ranar Laraba.

Kalaman nasu tamkar martani ne ga rahotannin da suka ambato shugaban riko na jam'iyyar ta APC, Maimala Buni, yana cewa Gwamna Matawalle shi ne jagoran APC a Zamfara bayan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar jim kaɗan bayan komawar Matawalle APC, ta ce ambato Mai Mala Buni yana cewa: "Daga yanzu Matawalle ne jagoran jam'iyyarmu mai girma a jihar Zamfara.

"Za ku saurari sauran shirye-shirye na samar da sabuwar jam'iyya daga wajensa nan gaba kaɗan," in ji Buni.

A lokacin da yake karɓar tutar jam'iyyar, Gwamna Matawalle ya karɓi jagorancinta a yayin da ya ayyana kansa a matsayin mamba a cikinta.

Kazalika Gwamna Matawalle ya shiga jam'iyyar ne tare da dukkan sanatocin jihar da ke kan mulki a yanzu, da ƴan majalisar wakilan tarayya shida daga cikin bakwai da kuma dukkan ƴan majalisar dokokin jihar.

'Ba za ta saɓu ba'

Sai dai Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa - wadanda gwamnan ya tarar a cikin jam'iyyar ta APC - sun ce ba za su yarda a yi musu hawan ƙawara ba.

"Abu guda ne ba mu yarda da shi ba, inda shi Gwamna Maimala ya ce [Matawalle ne jagoran APC] domin babu shi a cikin tattaunawarmu wadda muka yi da gwamnoni guda shida.

Abin da muka amince shi ne a je a kaddamar da Bello a dawo. Abin da muka amince a matsayin abin da za mu bayar a jam'iyya da abin da za mu dauka a gwamnati. Amma da muka je an yi takaddama mun tarar da an yi tsari in ji wasu cewa idan an je a rusa jam'iyya. Ba a rusa jam'iyya domin babu wanda yake da ikon rusa ta," in ji shi.

Shi ma Sanata Marafa ya ce nada Gwamna Matawalle a matsayin jagoran APC a Zamfara wata yaudara ce da ba za su amince da ita ba.

A cewarsa: "Mu rokonmu aka yi aka ce mu bari a yi abin da aka yi a Gusau. An dai yi biki ne kawai. Mu ne muka ce kafin a ce an zama daya sai an yi zaman [tattaunawa]. Amma wani ya zauna a Abuja ya ce ya rushe jam'iyya ya nada wani shugaba maganar banza da wofi ce."

Masu lura da lamuran siyasar jihar ta Zamfara dai na ganin komawar Gwamna Matawalle jam'iyyar APC za ta ta'azzara rikicin da ke cikin jam'iyyar musamman ganin yadda suka dade suna kai ruw rana da tsohon Gwamna Yari.

Da ma dai jam'iyyar ta APC ba ta dade da dinke barakar da ke tsakanin tsohon gwamnan Yari da kuma tsohon Sanata Marafa ba, wadda ta yi sanadin ya sa Kolin Kolin Najeriya ta kwace kujerr gwamnan jihar da ma sauran kujerun da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC aka bai wa jam'iyyar PDP.



Read full article

Source: BBC