BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Abin da sabuwar dokar haramta yaɗa hotunan batsa a Ghana ta kunsa

 121063347 Bbc Gwamnatin Ghana za ta hukunta duk wanda ya yaɗa hotuna ko bidiyon batsa na mata da yara

Wed, 13 Oct 2021 Source: BBC

Gwamnatin Ghana za ta hukunta duk wanda ya yaɗa hotuna ko bidiyon batsa musamman na mata da ƙananan yara, ƙarƙashin wata sabuwar doka.

Dokar na ƙunshe cikin kundin dokar tsaron intanet ta 2020, kuma za ta yi ƙoƙarin magance matsalar yadda ake yaɗa hotunan mutane na batsa wani lokaci da nufin tozarta wasu.

Babban jami'in ƴan sanda da ke kula da laifukan da suka shafi intanet na Ghana ACP Dr Gustav Herbert Yankson ya yi gargaɗi musamman ga mata, su daina tura wa maza hotunansu na batsa ko da kuwa mazajensu ne.

A cewar jami'in, hotunan za su iya faɗawa ga mugun hannu, musamman idan an sace wayar ko kuma an yi kutse.

Don haka, ko me zai zama illar tura hotunan tsaraicin wani saboda kuɗi, ko ɗaukar fansa ko don saboda wani dalili a intanet a Ghana?

Bisa sabuwar dokar da gwamnatin Ghana ta ƙaddamar, duk wanda aka kama ya yaɗa hotunan batsa na yara ko na manya zai iya fuskantar hukuncin ɗauri daga shekara biyar har zuwa 25.

Dokar kuma ta ƙunshi matakai kan cin zarafin yara ƙanana, inda mutum zai iya fuskantar ɗauri daga shekara biyar zuwa 15.

Wanda da ya yaɗa hotunan batsa a intanet ko kafofin sadarwa na ntanet, zai biya tara tsakanin dala dubu biyar zuwa dubu 10.

Barazanar yaɗa hotunan batsa saboda kuɗi

Haka kuma dokar ta fayyace cewa duk wanda ya yi wa wani barazanar zai yaɗa hotonsa ko bidiyonsa zai fuskanci fushin shari'a.

Hukuncin da za a yanke wa wanda ya yi wa wani barazana ya kai tsakanin ɗaurin shekara 10 zuwa 25 a gidan yari.

Yada hoton batsa da gangan

Sashe na 278 na dokar ya ce duk wanda ya yaɗa hotunansa na batsa ya aikata laifi da nuna rashin da'a.

Daga baya, jami'an Ghana za su shiga farautar mutanen da suka yaɗa hotunan da ke nuna tsaraici da gangan.

Wata da ta yi fice a Ghana, Akuapem Poloo ta fuskanci fushin doka inda aka ɗaure ta kan yaɗa wasu hotunanta da ɗata da ke nuna tsaraici a intanet.

Wata kotun Ghana ta taba yanke wa wata ƴar fim Rosemond Brown hukuncin ɗaurin watanni uku a gidan yari.

Kotun ta ce dalilin yanke hukuncin zai zama gargaɗi ne ga jama'a.



Read full article

Source: BBC