BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Abin da ya sa 'yan Koriya ta Kudu ba sa samun isasshen barci

Sleeping In Bed 8.jfif Wani da ke barci | Hoton alama

Mon, 11 Apr 2022 Source: BBC

Rashin samun isasshen barci na da tasiri sosai kan al'ummar kasar Koriya ta Kudu, saboda kasa ce da jama'arta ba su cika samun sukunin yin barci ba.

Ji-Eun ta far fuskantar matsalar rashin yin barci ne bayan da aikin da ta ke yi ya fara hana ta samun damar hutawa.

Akalla t akan yi aiki daga karfe 7 na safe har zuwa 10 na dare, amma a ranakun da aiki ke da yaa, matar mai shekara 29 da haihuwa kan ci gaba da yin aiki har karfe 3 na sanyin safiya.

Shugaban ofishin da take aiki kan kirata a tsakar dare domin y agaya ma ta wasu abubuwan da yake son ta yi na take.

"Na kasance kamar wadda ta manta yadda ake hutawa ma," inji ta.

A gundumar Gangnam ta masu hannu da shuni a birnin Seoul, akwai wani asibiti na musamman mai suna Dream Sleep Clinic, inda Likita Ji-hyeon Lee mai kwarewa kan halayyar dan Adam ke aiki, ta ce ta saba ganin mutanen da kan sha kwayoyin sa barci 20 cikin kowane dare domin kawai su iya runtsawa.

"A hankali barci kan zo wa mutum, amma 'yan Koriya na son bingirewa nan take, saboda haka ne suke shan magani," inji ta.

Sabo da shan magani ya haifar da wata matsala - matsalar dogara ga magani idan za a yi barci, wanda a halin yanzu ya zama annoba a kasar. Babu alkaluman yawan wadanda abin ya shafa amma ana kiyasta cewa akwai 'yan Koriya 100,000 da suka dogara ga shan kwayoyin sa barci kafin su iya yin barcin.

Idan suka kasa yin barci, su kan rika kwankwadar barasa bayan sun sha kwayoyin - halayyar da kan haifar da mummunan hadari ga rayukansu.

"Mutane kan rika yawo cikin yanayin barci. Su kan je firjinsu domin su ci abincin da suka adana a ciki ba tare da sun sani ba, ciki har da cin abincin da ba a girka ba," inji Likita Lee.

Ta saba ganin masu fama da matsananciyar matsalar rashin barci. Wasu maraa lafiyan kan gaya ma ta cewa sun shafe gomman shekaru ba su sami barcin da ya zarce na 'yan sa'o'i ba.

Ga yawan aiki ga tarin damuwa da rashin barci

South Korea is one of the most sleep deprived nations on earth. It also has the highest suicide rate among developed nations, the highest consumption of hard liquor and a huge number of people on antidepressants.

Tarihi ne zai sanar da mu dalilan da suka sa al'ummar wannan kasar suka sami kansu cikn wannan halin.

Cikin 'yan shekaru kasar ta bnkasa daga matsayin mataluciyar kasa zuwa matsayin wadda ta sami ci gaba matuka a fannin fashar zamani a tsakanin kasashen duniya.

Kasashe irin Koriya ta Kudu kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa na iya dogara ga tarin albarkatun da Allah ya ba su, amma Koriya ba ta da irin wadannan albarkatun. Ta sauya matsayar ta ne ta hanyar dagewa da kafewa kan inganta rayuwar al'ummar kasar.

Wannan ne yasa aka samar da wasu cibiyoyin da kan taimaka wa wadanda ke fuskantar matsalar rashin yin barci a kasar - inda ake kiyasta cewa 'yan kasar sun kashe kimanin dala biliyan 2.5 a shekarar 2019 kawai.

Kasuwar barci mai bunkasa

A birnin Seoul, akwai shaguna na musamman da ba sa sayar da komai sai kayan da suka jibanci barci. Tun daga zannuwan gado na musamman, zuwa ga fulullukan gado da magungunan taimaka wa mutum yin barci kamar jariri ake iya samu a shagunan.

Akwai kuma wasu shagunan masu samar da hanyoyin magance rashin barci ta hanyar amfani da fasahar zamani. A bara wani mutummai suna Daniel Tudor ya samar da wata manhaja mai suna Kokkiri domin taimaka wa masu matsala iya runtsawa - musamman matasa cikinsu.

Sai dai duk da cewa Koriya kasa ce ta yawancin mabiya addinin Bhudda, matasan kasar kan kalli natsuwa da lazimi a matsayin wani abin da tsofaffi ke yi, ba abin da ma'aikaci a ofis zai mayar da hankali kai ba.

Daniel ya ce wannan ne yasa ya shigar da natsuwa da lazimi daga addinin Bhudda zuwa wannan manhaja.

Hyerang Sunim mai yi wa addinin Bhudda hidima ne a wani kebabben wurin ibada da ke wajen birnin Seoul, wurin da masu fama da wannan matsalar kan tafi domin samin waraka ta hanyar amfani da koyarwar addinin na Bhudda.

A shekarun baya, wadanda suka yi ritaya daga aiki ne ke zuwa irin wadannan wuraren ibadan domin yin lazimi ko samun natsuwa. Amma sai ga shi matasa ma'aikata na ziyartar su. Sai dai ana sukar wadannan wuraren ibadan da ribata daga matsalolin da mutane ke fuskanta.

"Lallai akwai masu nuna damuwarsu... amma ina ganin kuma akwai fa'idoji," inji Hyerang Sunim.

Ana bukatar sauyin alkibla

Wata 'yar Koriya ta Kudu mai suna Lee Hye-ri da ta taba halartar irin wadannan wuraren ibada na addinin Bhudda bayan da matsalar rashin barci ta tsananta, ta ce ta gano hanyar kulawa da matsalar da kanta.

"Komai ya rataya a wuyana ne, wato dukkan matsaloli daga gare ni suka samo asali. Abin da na koyo a nan ke nan."

Sai dai mayar da matsalar ta zama ta wanda ke faama da ita ne kawai na iya haifar da wata matsalar ta daban.

Wasu na ganin za a sami wata matsalar ta dora wa kai laifi. Suna ganin magance matsalar ta hanyar yin lazimin addinin Bhudda ya yi kama da manna wa matsalar filasta - wadda ita kadai ba za ta iya warkar da matsalar ba.

Suna cewa sai an sauya yadda kasar ta ke tursasa wa jama'arta a wuraren aiki kafin a magance matsalar.

Daga baya matsalar rashin barcin da ke damun Ji-Eun ta kai ga sai da ta daina aikin da ta ke yi. A yanzu ta koma yin wani aikin da babu matsi sosai kuma wanda ake tashi da wuri, sannan saboda annobar korona, tana iya yin aiki daga gida. Ta ce ita ma ta ziyarci asibitin Likita Lee domin neman maganin matsalar rashin barcin da ke damunta.

"Ina fa'idar yin aiki tukuru yanzu da kasarmu ta sami gagarumin ci gaba?" inji Ji-Eun. "Ya kamata a e muna iya shakatawa da natsuwa sosai."



Read full article

Source: BBC