BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Abu biyar da suka ja aka cire Faransa daga Euro 2020

 119132391 Gettyimages 1233708203 594x594 Paul Pogba tare da Kylian Mbappe

Tue, 29 Jun 2021 Source: BBC

Masana kwallon kafa na ci gaba da sharhi kan fitar da Faransa daga gasar kasashen Nahiyar Turai ta 2020.

Sun bayyana wasu dalilai guda biyar da suke ganin sune suka janyo aka cire Fraansa daga gasar.

Abubuwan da suka faru a wasannin da suka gabata tsakanin Netherland da Greece da kuma tsakanin Belgium da Portugal mai rike da kwofin ya bai wa Switzerland kwarin gwiwar cewa za su iya cinye Faransa.

Duk da cewa ita ce ke rike da kofin duniya kuma take a matsayi na biyu na jerin kasashen da suka fi ko wadanne kyau a duniya, amma hakan bai hana a cire su ba.

Wata dabara da suka kara amfani da ita kuma shi ne hana Faransa taka ledar da suka saba a lokutan wasansu, salon da Faransa ke yi shi ne na kai kora ta gefunanta da kuma taba kwallo da take yi cikin hanzari.

Switzerland ta rika take manyan 'yan wasan Faransa a matsayin wata dabarar wasa da za ta fusata 'yan wasan Faransa da ita, ta rika take 'yan wasa irinsu Pogba da Rabiot da sauransu.

Farke kwallayen da Switzerland ta rika yi akai-akai ta kara kashewa Faransa jiki, hakan ya sanya su kokarin gwada kwallon da ba ita suka saba yi ba ta, wanda kuma itama ta ki yiwuwa.

Kwarin gwiwar da Switzerland ta samu bayan ta fara farke kwallonta ya sanya ta jin cewa za ta iya cire Faransa daga gasar Euro kamar yadda ya faru.

Wasa daya Faransa ta yi rashin nasa a cikin wasanni 17 da ta buga a gasar kasashen Turai da ta cin kofin duniya, wasan da Portugal ta cinye su a 2016.

Wannan dalili ya sanya mafi yawan masu sharhi da BBC ta yi magana da su, suka bai wa Faransa nasara a wasan.



Read full article

Source: BBC