BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Abubuwan da za mu iya koya daga mutum-mutumin kasar Japan

Japanese Flag Tutar kasar Japan

Mon, 30 Aug 2021 Source: BBC

A wani wurin ibada mai shekaru 400 na mabiya addinin Buddha, masu ziyara na iya yawo ta cikin lambunan shakatawa mai duwatsu, su zauna cikin kwanciyar hankali suna shan gahawa, kana suna daukar darussan addinin Buddha daga wani limami da ba a saba gani ba: wani mutum-mutumi da ake kira da suna Mindar.

Yana da wata irin fuska mai kwantar da hankali da kuma kamanni wanda ba za a iya rarrabewa ba, ba na tsoho ba ba kuma na yaro ba, ko kuma mace ko namiji.

Baya ga fata ta mai kama da ta gaske da ta rufe daga kanshi zuwa saman jikinsa, yana nuna rashin kammaluwarsa wanda ke bayyana wasu injina da bututai daga ciki. Amma Mindar yana da nagarta sosai, yana magana a kan wasu rubutattun kalamai na addinin Buddha masu wahalar ganewa da ake kira Heart of Sutra.

Idan kana so ka gano inda za a samu wani limamin mutum-mutumi, kawai kana bukatar yin tunanin cewa a kasar Japan ne, a wani wurin ibada na Kodai-ji mai matukar kyau a birnin Kyoto.

An dade da sanin Japan a matsayin kasar da ke kerawa tare da yin mu'amala da mutum-mutumi sosai fiye da komai.

Yayin da ake yawan zuguguta wannan suna da Japan din ta yi a kasashen waje - gidajen 'yan kasar ta Japan da shaguna ko kamfanoni ba su cika da mutum-mutumin ba kamar yadda labarai a manyan shafukan jaridu ke nunawa ba - akwai wani abu daban game da hakan.

Abubuwan yau da kullum

Wasu masu sa ido na kasar Japan sun ce addinin gargajiyar kasar, Shinto, ya bayyana yadda yake kaunar mutum-mutumi.

Shinto wani yanayin amfani da tsirrai ne da ake dangantawa da ruhi ko kami, ba ga mutane kadai ba har ma ga dabbobi, da abubuwan dake kewaye da mutane kamar tsaunuka, har ma da abubuwa kamar fensira.

"Ko wane abu yana da rai,'' a cikin kalaman Bungen Oi, limamin limamai na wurin ibadar mabiya addinin Buddha da ke yi wa mutum-mutumin karnuka jana'iaza.

Kamar yadda wannan ra'ayi yan una, babu wani banbanci tsakanin mutane, da dabbobi, da kuma abubuwa, don haka ba wani abin al'ajabi ba ne don mutum-mutumi ya nuna halayya irin ta dan adama - yana kawai nuna irin na shi ruhin ne.

"Ga 'yan kasar Japan, muna iya ganin abin bauta a cikin wani abu," in ji Kohei Ogawa, jagoran wadanda suka kera Mindar.

Tsarin amfani da tsirrai wajen bauta na cin karo da falsafar al'adaun Yammacin duniya.

Mutanen Girka ta zamanin da suna da al'adar amfani da tsirrai a fannin yadda suke ganin rauhanai a wurare kama koramu, amma kuma suna tunanin ruhin bil adama da tunaninsu a matsayin badan daga sama da sauran halittu da abubuwa da ke kewaye.

Addinan Musulunci, da na Kirista da kuma na Juda na saka mutane a babban matsayin na kasancewa halittar Ubangiji mafi girma da daraja.

An kuma gargadi Yahudawan zamanin baya kan bayar da muhimmanci ga abubuwa, don kada su zama masu bauta wa gumaka, wanda dokoki goma da Ubangiji ya saukar wa Annabi Musa suka haramta.

Addinin Musulunci ya haramta bautar gumaka da ma kera duk wani abu mai kama da dabba ko kuma mutum.

Kada ku yi wa halittun Ubangiji shisshigi

Kamar yadda al'adun ta tunanin Yammacin duniya suna nuna, duk wani inji da zai rika yin abubuwa kamar na dan adam, ya zama saba wa tsarin iyakar halittu.

Wannan gargadi game da dabi'a na nuni da sanannen abu a tarihi game da fasaha, kamar Frankenstein, wanda ya samo akasarin sakonnin ciki na halayya ta gari daga littafin Bible, in ji Christopher Simon, wani farfesan kwatanta al'adu a Jami'ar Addinin Kirista a birnin Tokyo.

"Dr Frankenstein ya kirkiri rayuwa a jikin wani dodo. Kamar wasu mutane da cin 'ya'yan bishiyar ilimi a lambun Eden. Wannan shi ne ainihin aikata sabo; a sakamakon haka, aka hukunta mu," in ji shi.

A karshen labarin marar dadi, bayan da Dakta Frankenstein da dodon na shi duka suka mutu: "Ku yi taka-tsan-tsan mutane. Kada ku ce za ku dauki matsayin Ubangiji."

Wasan Jamhuriyar Czech na shekarar 1920 RUR, wanda ya gabatar da kalmar ''robot'' wato mutum-mutumin da aka yi wa taken addini: daya daga cikin 'yan wasan ya kirkiri mutum-mutumin da ke tabbatar da cewa babu ubangiji, yayin da dayan kuma ya ce ya kamata a ce mutum-mutumi na suna da ruhi, kana mutum-mutumi biyu da suka fara soyayya aka labaka musu suna "Adam" da "Eve" wato "Hauwa'u" da ''Adamu''.

A karshen labarin, mutum-mutumin sun hallaka kowa ban da daya.

Direban masana'anta

Wasu masana sun ce tushen mahangar fasahar Japan musamman mutum-mutumi suna da tarihi maimakon addini da kuma falsafa.

A shekarun da suka gabata bayan yaƙin duniya na biyu, Japan ta mayar da bunƙasar fasaha ba wai kawai gina tattalin arziki ba har da ƙimarta

"Mutumin-mutumin sun taka muhimmiyar rawa domin wajen farfaɗo da tattalin arziki wajen 1960," in ji Martin Rathmann malami a jami'ar Siegen ta Jamus.

"Maimakon sassauta tsauraran matakan shige da fice domin taimakawa ƙarancin ma'aikata, sun ƙirƙiri fasahohi da dama ta hanyar mutum-mutumi." Wannan ya taimaka wajen bunƙasa ayyuka, inda Japan ta zama babbar mai samar da mutum-mutumi zuwa ƙasashen duniya.

A 1969, shugabannin sojin Japan, sun haramta yin amfani da fasaha domin samar da sabbin makamai don hana haifar da sabbin abokan hamayya, a cewar binciken Cosima Wagner na Jami'ar reie Universität da ke Berlin.

Masu ƙirƙira sun koma samar da wasu mutum-mutumin da za a riƙa amfani da su a ɗakunan taro da wurin shan gahawa.

Duk da cewa an daina yayin mutum-mutumin gwaji a lokacin da aka shiga ƙarni na 20, an ci gaba da amfani da su a matsayin kayan wasa.

Lokacin da Masahiro Mori, shahararren masani kan mutum-mutumi ya ƙirkiri kalamar "uncanny valley", ya fara bincike kan mutum-mutumi a shekarun 1970 ya fahimci cewa da wuya a ɗauke su da muhimmanci.

Kalaman na nufin 'halin ba daɗi da muke shiga idan muka gamu da abubuwa masu kama da mutum'.

"A wancan lokacin, mutane na ganin bai dace jami'o'i su riƙa bincike kan mutum-mutumi ba," ya ce a wata tattaunawa da mujallar IEEE Spectrum.

"Suna ganin ɓata lokaci ne a zauna ana aiki kan abin wasa."

Bayan da aka gama yaki a japan, mutane sun riƙa kallon mutum-mutumi a matsayin abu mai kyau, sannan ya zama wani abu mai ɗaukar hankali. Su kuwa ƙasashen Yamma ba su mayar da hankali ba a kan batun.

Amurka, wadda a lokacin Yakin Cacar Baka ya ɗauke wa hankali, ta zuba kuɗi masu yawa wajen samar da mutum-mutumi don amfanin soji.

Manga super-star

Waɗannan rarrabuwar ra'ayi kan fasaha sun bayyana a ɓangaren nishadi a ƙarshen ƙarni na 20.

Astro Boy ya shahara a fina-finai da littafai da sauran kayan amfani a Japan a shekarar 1952.

Astro Boy wani mutum-mutumi ne da ke amfani da wata ɓoyayyar baiwarsa wajen taimakon ƙasarsa da yaɗa labari masu amfani kan fasaha.

"A cewar wanda ya ƙirƙiri Astro Boy, Osamu Tezuka, an tursassa masa bayyana fasaha a matsyain abu mai kyau ne... inda kamfanin da ke wallafa labaransa da masu karatu suka sa haka don samar da wani kyakkayawan fata ga ƴan Japan waɗanda a shekarun 1950 suke cikin damuwar yaƙi.

"Sakon Tezuka hanya ce ta nuna ba a fahimci halayyar ɗan Adam ba."

Saƙon ya yi tasiri kan ƴan Japan musamman waɗanda a yanzu suka ƙiƙiri nasu mutum-mutumin.

"Tun daga makarantar sakandire sun ta mafarkin Astro Boy kuma sun zama masu samar da mutum-mutumi saboda shi."

Ƙasashen Yamma su ma suna da labarai masu amfani kan mutum-mutumi, amma waɗanda suka fi tasiri su ne labarai kan barazanar da suke yi ga mutane.

Fargabar da kasashen Yamma ke da ita kan mutum-mutumi ta fito karara a jerin fina-finan Terminator, inda komfutar tsaro ta SkyNet ta zama mai ruhi, mutane suka yi koƙarin kashe ta kuma SkyNet ta yi amfani da android mai suna Terminator wajen fara yaƙi da su.

A wani bangaren, Japan da ba ta da tsoro game da aruwar amfani da mutum-mutumi ta ƙagu ta yi amfani da su don samar da ma'aikata a ƙasarta da ke da ƙarancin ma'aikatan, don yin ayyuka kamar kula da tsoffin ƙasar da ƙaruwa kullum.

Gwamnati da sana'o'i na nema a riƙa amfani da mutum-mutumi don taimaka wa tattalin arziƙi da bayar da gudunmuwa ga ƙasar.

Sai dai daga ƙarshe ko ƴan Japan ma za su fi so a ce mutane ne ke yi masu aiki.

""Idan na yi tafiya a Japan, na gano cewa wuraren kula da marasa lafiya a Japan ba su da yawan mutum-mutumi," a cewar Marketta Niemel wata mai bincike. "An fi son mutane a madadinsu."

Astro Boy ya ba Japan wani fata mai kyau kan amfani da mutum-mutumi nan gaba. Har yanzu 'yan Japan na da wannan kyayawan fatan.



Read full article

Source: BBC