BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Akwai rahin tabbas game da makomar Steve Cooper a Nothingham Forest , Bayer Leverkusen na zawarcin Xabi Alonso

Ba40df10 4441 11ed B131 570b90286fb7 Steve Cooper

Wed, 5 Oct 2022 Source: BBC

Mamallakin kungiyar Nottingham Forest Evangelos Marinakis na tunanin korar kocin kungiyar Steve Cooper da wasu ma’aikata sakamakon rashin nasara sau biyar a jere a gasar Firimiya. (Mail)

Kungiyar ta Forest na kuma tunanin daukar tsohon  kocin Liverpool Rafael Benitez a matasyin wanda zai maye gurbin Cooper, shi ma tsohon kocin Burnley Sean Dyche na cikin wadanda ake tsamanin za ta dauka. (Guardian)

Ita kuwa Manchester United  ba ta son barin dan wasan  gaban Portugal Cristiano Ronaldo ya tafi a kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu kuma mai yiwuwa dan wasan mai shekara 37 ya jira har sai kwantigarinsa ya kare a bazara mai zuwa kafin ya bar Old Trafford . (Mirror)

Tsohon kocin Chelsea Thomas Tuchel ya yi watsi da damar da aka ba shi ta zama kocin Bayer Leverkusen a kasar haihuwarsa, Jamus . (Sport1)

Haka kuma Bayer Leverkusen na duba yiwuwar  nada  tsohon dan wasan tsakiyar Liverpool da Bayern Munich da kuma Real Madrid Xabi Alonso a matsayin wanda zai maye gurbin kocinta Gerardo Seoane. (ESPN)

Chelsea ce ke kan gaba wajan neman dan wasan gaban AC Milan Rafael Leao mai shekara 23 dan wasan kasar Portugal (Star)

Watakila AC Milan ta yi amfani da wasanta  da Chelsea a gasar cin kofin zakarun Turai don tattaunawa da Blues.

Watakila AC Milan ta yi amfani da wasanta da Chelsea a gasar cin kofin zakarun Turai don tattaunawa da Blues kan sayen dan wasan baya na Ingila Trevoh Chalobah mai shekara 23 da dan wasan gaban Amurka Christian Pulisic, mai shekara 24.  (Calciomercato - in Italian)

Inter Milan za ta yi kokarin dauko dan wasan tsakiyar Netherlands Donny Van de Beek mai shekara 25  daga Manchester United a watan Janairu . (Fichajes - in Spanish)

Shugabannin kungiyar Liverpool a shirye suke su bayar da makudan kudade don sayan manyan yan wasa a watan Janairu idan kocin Reds Jurgen Klopp da masu daukar ma’aikata na kungiya sun sami yan wasan da suka dace (Football Insider)

Har illa yau kocin Liverpool ya ce yana son  sayan dan wasan tsakiya  na Arsenal Martin Odegaard mai shekara 23 a lokacin da yake Borussia Dortmund sai dai dan wasan Norway ya zabi Real Madrid. (Goal)

Arsenal na tunanin ba dan wasan tsakiyar Belguim Albert Sambi Lokonga mai shekara 22 wata yarjejeniyar musaya da dan wasan Juventus kuma dan wasan tsakiyar Italiya Manuel Locatelli (Calcio Mercato Web)

Leandro Trossard mai shekara 27,  ya ki ya musanta rade radin da ake yi a kan cewa yana son  ya bar Brighton  yayin da Arsenal da Chelsea sun nuna suna son dan wasan Belguim ya taka mu su leda. (Mail)

 

Everton za ta yi amfani da zabin mayar da aro na dan wasan bayan Ingila Conor Coady mai shekara 29 daga Wolverhampton  Wanderers zuwa na dindindin kan farashi kasa da fam miliyan 10  (Times - subscription required)

Kocin Chelsea Graham Potter ya ce abin da ya fi maida hankali shi ne ganin  dan wasan tsakiyar Faransa N’Golo Kante ya sake samun lafiya  kuma  batun kwantiragin dan wasan mai shekara 31 wanda zai zo karshe a bazara mai zuwa magana ce da ke tsakanin kungiyar da shi. (Guardian)

Sevilla ta cimma matsaya da  tsohon kocinta Jorge Sampaoli a kan ya koma kungiyar domin maye gurbin Julen Lopetegui  a matsayin shugaba. (ESPN)



Read full article

Source: BBC