BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Al-Ahli na neman yi wa Man United zagon kasa kan Amrabat

59d54870 2fda 11ee 8f52 Fbf70e4bf742 Sofyan Amrabat

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Al-Ahli ta Saudi Arabiya na zawarcin dan wasan tsakiya na Fiorentina Sofyan Amrabat, wanda aka alakanta shi da komawa Man Utd.

Ana sa ran cewa Manchester United za su mayar da Amrabat kan gaba cikin jerin sunayen 'yan wsan sda suke bukata bauayn sun kammala siyan dan wasan gaba na Atalanta Rasmus Hojlund.

Rahotanni sun bayyana cewa Hojlund na dab da komawa kungiyar ta Premier kan kudi kusan fam miliyan 73. Yana shirin bin sahun Mason Mount da Andre Onana a Old Trafford.

Ana yi tunanin cewa farashin Amrabat zai iya kaiwa kusan fam miliyan 30 kuma zai iya zuwa don ba da gasa ga Casemiro

Ten Hag ya san dan wasan na Morocco da kyau bayan ya horar da shi a Utrecht.

Dan wasan wanda haifaffen Netherlands ne ya buga wasanni 50 a karkashin Ten Hag, inda ya zura kwallo daya kuma ya taimaka aka zura kwallaye goma.



Read full article

Source: BBC