BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Al Ahly ta lashe Champions League na 10 jumulla

 119478614 369e1e9c 2f10 4b28 B287 67767a4eff68 Al Ahly ta yi nasarar doke Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu 3-0 ranar Asabar a Morocco

Mon, 19 Jul 2021 Source: BBC

Kungiyar Al Ahly ta Masar ta lashe kofin Zakarun Afirka wato Champions League na 10 jumulla.

Al Ahly ta yi nasarar doke Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu 3-0 ranar Asabar a karawar da suka yi a Morocco.

Kungiyar ta Masar ta fara cin kwallo ne ta hannun Mohamed Sherif, bayan da suka koma zagaye na biyu, sai Mohamed Magdi Kafsha ya kara na biyu minti 11 tsakani, sannan Amr Al Sulaya ya ci na uku kasa.

Kocin Al Ahly, Pitso Mosimane ya dauki kofin Champions League uku da kungiyar Masar, har da wanda ya lashe a bara da kuma wanda ya doke Mamelodi Sundowns a 2016.

Kungiyar da ke Soweto wadda karon farko ta kai wasan karshe a Champions League ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 cikin fili, bayan da aka bai wa Happy Mashiane jan kati.

Da wannan sakamakon Alhali ta lashe kofin Zakarun Afirka na 10 jummala da tazarar biyar tsakaninta da TP Mazembe da El Zamalek masu biyar-biyar kowacce.

Jerin kungiyoyin da suka lashe Champions League na Afirka:

  • Al Ahly 10


  • TP Mazembe 5


  • El Zamalek 5


  • Esperance ST 4
  • Raja Club Athletic 3


  • Canon Sportif de Yaounde 3


  • Hafia Conacry 3


  • Wydad Athletic Club 2


  • Entente Sportive de Setif 2
  • Enyimba International FC 2


  • JS Kabylie 2


  • Asante Kotoko 2




  • Read full article
    Source: BBC