BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

An kai wa jirgin ƙasa hari a hanyar Kaduna

Nigeria Kaduna Map Kaduna wata jiha ne a arewacin Najeriya

Mon, 28 Mar 2022 Source: BBC

Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga sun tayar da bam a titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da ke ɗauke da fasinja 970.

Rahotanni sun ce maharan sun yi nasarar hana jirgin tafiya, inda suka buɗe wuta.

Ɗaya daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin ya tabbatar wa BBC da harin, inda ya ce maharan sun kwashi mutane sun tafi da su. Sannan jami'an tsaron da ke cikin jirgin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar.

Ya ce sun kashe mutum guda.

Wani ma'aikacin tashar jirgin a Rigasa ya shaida wa BBC cewa "jirgin ya kamata ya iso misalin ƙarfe 8:20 amma har yanzu ba labari."

Hukumomin sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya da hukumomin gwamnatin Kaduna ba su tabbatar da al'amarin ba.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: