BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

An tsare dan uwan Pogba kan hada baki a karbi kudin dan wasan Juve

6b457f90 37d2 11ed 87f1 2932dec4b170 Paul tare da Mathias Pogba

Mon, 19 Sep 2022 Source: BBC

Ana tsare da Mathias Pogba ana kuma bincikensa da tuhumar karbar kudi daga dan uwansa, Paul Pogba da hada kai da wata kungiyar masu aikata laifi.

Ana kuma tsare da wasu mutum hudu kan tursasa karbar kudin kamar yadda aka sanar da kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Sai dai lauyan Mathias Pogba, mai suna Yassine Bouzrou, ya ce wanda yake wakilta bai aika wani laifi ba.

Mathias Pogba, mai shekara 32, ya tabbatar cewar muryarsa ce a wani bidiyo a yanar gizo a watan jiya da ke yin alkawarin bankado wasu abubuwan kunya kan Pogba da ake ta boyewa.

Masu shigar da kara a Faransa na kan bincike tun farkon watan nan, bayan da Paul, tsohon dan kwallon Manchester United ya ce yana shan barazana daga wata kungiyar masu aikata laifi.

Tun a ranar 16 ga watan Yuli ya kai korafi ga jami'an tsaro a birnin Turin da cewar ana masa barazanar sai ya bayar da £11.29m.

Paul, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Faransa a 2018 a Rasha, ya bar Old Trafford a bana, bayan da yarjeniyarsa ta kare a karshen kakar da ta wuce.

Mathias Pogba, wanda kwararren dan wasa ne ya wakilci tawagar Guinea ya kuma taka leda a kungiyoyi da yawa a Turai da suka hada da Crewe da Wrexham da Crawley da kuma Partick Thistle.



Read full article

Source: BBC