BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Arsenal ta kammala daukar Albert Sambi Lokonga daga Anderlecht

 119490061 Gettyimages 1329524066 Albert Sambi Lokonga ya koma Arsenal daga Anderlecht

Mon, 19 Jul 2021 Source: BBC

Arsenal ta kammala daukar matashin dan kwallon Belgium, Albert Sambi Lokonga daga Anderlecht kan yarjejeniya mai tsaho.

Ba a fayyace kudin da aka sayi dan kwallon ba, amma ana hasashen cewar ya kai dalar Amurka miliyon 17.2.

Ya koma Anderlecht yana da shekaru 15, kuma Lokonga ya fara yin tamaula a kungiyar cikin watan Disambar 2017, wanda kawo yanzu ya yi karawa 78 da cin kwallo uku.

Mai taka leda daga tsakiya wanda zai saka riga mai lamba 23 dauke da sunan Sambi, ya buga wa tawagar Belgium wasa ta matasa 'yan kasa da shekara 21 ya ci kwallo biyu.

Dan kwallon zai je ya hadu da 'ya wasan Gunners, bayan da ya killace kansa, kamar yadda doka ta tanada ga duk bakon da ya sauka Burtaniya, don gudun yada cutar korona.

Arsenal ta kammala daukar dan kwallon Brighton, mai tsaron baya, Ben White kan fam mi;iyan 50 da kuma Nuno Tavares daga Benfica kan fam miliyan takwas.



Read full article

Source: BBC