BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Arsenal ta soke zuwa gasar da za ta buga a Amurka

 119524397 Mediaitem119523259 Mikel Arteta, kocin Arsenal

Thu, 22 Jul 2021 Source: BBC

Arsenal ta soke zuwa Amurka, domin shiga gasar da za ta bata damar shirin tunkarar kakar bana,, bayan da wasu daga cikin 'yan tafiyar suka kamu da cutar korona.

Tun farko an tsara cewar Gunners za ta buga wasannin a Florida, inda za ta fafata da Inter Milan da Everton da kuma Millonarios ta Colombia.

Arsenal ba ta fayyace yawan wadanda suka kamu da annobar ba, ba ta sanar ko 'yan wasa suna daga cikin wadanda suka kamu da cutar ba.

Kungiyar ta sanar cewar ''Wannan matakin da ta dauka ya zama wajibi don kare lafiyar 'yan wasa da jami'an kungiyar.''

An tsara fara gasar Florida Cup ranar Lahadi da za a kara a Camping World Stadium a Orlando, sai dai kawo yanzu mahukunta wasannin ba su sanar ko za su maye gurbin Arsenal da wata kungiyar ba.



Read full article

Source: BBC