BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Atletico ta dauki Rodrigo de Paul daga Udinese

 119363549 Rodrigodepaul Rodrigo de Paul zai koma Atletico Madrid

Tue, 13 Jul 2021 Source: BBC

Wadda ta lashe kofin La Liga, Atletico Madrid ta kammala daukar Rodrigo de Paul daga Udinese kan kwantiragin kaka biyar ta tamaula.

Sai dai Atletico ba ta fayyace kudin da ta sayo dan kwallon ba, amma wasu kafar yada labarai a Burtaniya sun ce kudin ya kai Yuro miliyan 35, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 41.50.

De Paul dan kwallon tawagar Argentina, mai shekara 27, ya buga wa kasar karawa biyar a Copa America, shine ya bai wa Angel Di Maria kwallon da ya ci Brazil, suka lashe kofin bana.

Ya taka rawar gani a Udinese a kakar 2020-21, wanda ya ci kwallo tara ya kuma bayar da 10 aka zura a raga a karawa 36 da ya yi a gasar Serie A ta Italiya.

De Paul ya yi kaka biyar a Italiya, tun bayan da ya koma Udinese a 2016, ya kuma buga wasa 184 a dukkan fafatawa da cin kwallo 34, ya kuma bayar da 36 aka zura a raga.

Ya kuma taka leda a gasar La Liga a Valencia tsakanin 2014 zuwa 2016.



Read full article

Source: BBC