BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Bincike ya gano cewa iyalan amarya na biyan maƙudan kuɗi duk da haramta ba da sadaki a Indiya

 119157090 Gettyimages 494070628 594x594 1 A Indiya, iyalan amarya kan biya makudan kudi matsayin sadaki

Wed, 7 Jul 2021 Source: BBC

Kuɗin sadaki da ake biya a Indiya ya rage yin tashin gwauron zabi a 'yan shekarun da suka gabata, a cewar wani bincike na Bankin Duniya.

Masu binciken sun nazarci aure 40,000 da aka yi a ƙauyukan Indiya daga sheakarar 1960 zuwa 2008.

Sun gano cewa an biya sadaki a kashi 95 cikin 100 a ƙasar duk da cewa doka ta haramta hakan tun 1961.

Biyan sadakin wanda ake siffanta shi da rashin tausayi, an ci gaba da yin sa, abin da yake jawo wa cin zarafi da kuma kisa a wani lokacin.

Biya da kuma karɓar sadaki al'ada ce ta tsawon shekaru a nahiyar Kudancin Asiya, inda iyayen amarya ke bai wa iyayen ango tsabar kuɗi da tufafi da kuma kayan kwalliya.

An samo binciken ne daga bayanan biyan sadaki na jiah 17 na Indiya da suka ƙunshi kashi 96 cikin 100 na al'ummar ƙasar baki ɗaya. Ya mayar da hankali kan ƙauyukan Indiya saboda mafi yawan jama'ar ƙasar na zaune ne a karkara.

Masana tattalin arziki, S Anukriti da Nishith Prakash da Sunghoh Kwon, sun tattara bayanai game da darajar kayan da ake bayarwa a matsayin sadaki - kuɗi ko kaya - wanda aka bayar ko aka karɓa a lokacin aure.

Sun duba jumillar sadakin wanda iyalan amarya suke bai wa ango ko kuma na ango suke bai wa na amarya. Binciken ya gano cewa a lokuta 'yan kaɗan ne sadakin da iayalan ango ke bayarwa ya ɗara na wanda na amarya ke bayarwa.

Sun kuma gano adadin tsakatsaki na sadakin ya daina tashi sosai a tsawon lokaci, yayin da ya ɗan tashi kafin shekarar 1975 da kuma bayan 2000.

Kazalika, sun fahimci cewa iyalan ango na kashe rupee 5,000 - kwatankwacin N27,000 - adadi na tsakatsaki na kyautuka da suke bai wa iyalan amarya.

Abin mamaki, kayan da iyalan amarya ke bayarwa sun ninka sau bakwai da kusan rupee 32,000 - kwatankwacin N177,000. Hakan na nufin suna biyan jumillar kuɗi da kaya na sadaki kimanin 27,000.

Sadaki na lashe kaso mai yawa na arzikin iyali: a 2007, sadaki na tsakatsaki a ƙauyukan Indiya bai wuce kashi 14 cikin 100 ba na kuɗin da iyalai ke samu.

"A matsayinsa na wani ɓangare na arzikin iyali, farashin sadaki ya sauko saboda samun mutanen ƙauye ya ƙaru a Indiya," a cewar Dr Anukriti, wani masanin tattalin arziki da aiki da Sashen Bincike na Bankin Duniya.

"Amma dai wannan hasashe ne kawai - idan ana son sanin haƙiƙanin farashin sadaki game da arzikin da iyalai ke samu, sai mun samu bayanan abin da kowane gida ke samu, sai dai babu waɗan nan bayanan a yanzu," in ji shi.

Aure a Indiya



  • Kusan kowane gidan aure a Indiya mace ɗaya ce a gidan
  • Ƙasa da kashi 1 cikin 100 ne ake yin saki a cikinsu


  • Iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen zaɓar miji ko mata - a kashi 90 cikin 100 na auren da aka yi daga 1960 zuwa 2005, iyaye ne ke zaɓar miji ko mata


  • Fiye da kashi 85 na mata na auren wani wanda ba ɗan ƙauyensu ba


  • Kashi 78.3 na aure ana yin su ne a unguwa ɗaya
  • Majiya:

    Marriage Markets and the Rise of Dowry in India

    wanda Gaurav Chiplunkar da Jeffrey Weaversuka wallafa

    Binciken har wa yau, ya gano cewa kusan mabiya kowane addini a Indiya na biyan sadaki. Kiristoci da Sikhs "na biyan sadaki yanzu sosai", abin da ya sa suka zarta 'yan Hindu da Musulmai.

    Cikin wani bincike da aka wallafa a Janairu, masana tattalin arziki Gaurav Chiplunkar da Jeffrey Weaver sun yi amfani da bayanai na fiye da ma'aurata 74,000 a ƙarnin da ya gabata don gano yadda biayn sadaki ke sauyawa a tsawon lokaci.

    Sun yi ƙiyasin cewa jumillar kuɗin sadakin da aka biya a Indiya daga 1950 zuwa 1999 ya kai kusan dala biliyan 500.



    Read full article

    Source: BBC