BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Boko Haram: 'Mutum kusan 350,000 suka mutu sanadin rikicin kungiyar'

Boko Haram Distributions 3 Mutum kusan 350,000 suka mutu saboda hare-haren yan Boko Haram, inji wani rahoto

Thu, 1 Jul 2021 Source: BBC

Wani sabon rahoto da Shirin Raya Kasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) wato UNDP ya fitar ya ce mutum kusan 350,000 ne suka mutu cikin shekara 12 a arewa maso gabashin Najeriya sanadin rikicin Boko Haram.

Rahoton ya ce fiye da kashi casa'in cikin dari na mutanen da suka mutu kananan yara ne.

Shirin ya kara da cewa kisan duk mutum daya kai tsaye sakamakon rikicin, na daidai da rashin mutum tara saboda tasirin yakin.

UNDP ya ce adadin ƙananan yara da za su mutu zai iya kai wa miliyan ɗaya nan da shekara ta 2030 idan ba a shawo kan rikicin ba.

UNDP ya kara da cewa yara 170 ne suka yi ta mutuwa a kowace rana a Najeriya a shekarar 2020 da ta wuce sakamakon rikicin Boko Haram da ake fama da shi a arewa maso gabashin kasar.

A cewar rahoton, yawan kananan yaran da ke mutuwa a yankin zai iya kai wa 240 a kowace rana nan da zuwa shekara ta 2030.

Lamarin kamar yadda Shirin na raya ƙasashe na MDD ya bayyana, ya fi shafar yara masu rauni `yan kasa da shekara biyar, waɗanda ke fama da yunwa da kuma cutuka sakamakon karancin ruwan sha mai inganci.

Yanayin rikicin, musamman yadda ya ki ci ya ki cinyewa, sannan kuma ake mirginawa da shi daga wata shekara zuwa wata, yana mummunan tasiri a kan kananan al'umma musamman yara.

Baya ga kuncin rayuwa da ake shiga sakamakon tilasta wa al`umma barin gidajensu da rikicin ke yi, rashin samun isasshiyar kulawa a bangaren kiwon lafiya na cikin abubuwan da ke sanadin mutuwar yara a wannan yanki da ke fama da rikici.

Rahoton, wanda aka masa take da "kididdigar tasirin rikici a kan haba da bunkasar shiyyar arewa maso gabashin Najeriya", ya hararo cewa za a samu koma-baya ta fuskar tattalin arziki, da ilimi.

Sai kuma masifar mutuwar jarirai da kananan yara da kuma karancin abinci mai gina jiki.

Har wa yau, Shirin Raya Kasashe na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya kiyasta cewa rikicin da ake fama da shi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar ya tilasta wa dalibai ko 'yan makaranta miliyan daya da 800 barin karatu.

Kuma wannan lamari, kamar yadda majalisar dinkin duniyar ke cewa yana da munin gaske, kana ta bukaci gwamnati ta gaggauta daukar mataki a kansa.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: