BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Boko Haram: Sojin Najeriya sun yaye sama da mayaƙa 500 kan sana'o'i da dama

 123676659 B7a280f1 B39c 45b7 84b8 3121280a00ba Sojojin Najeriya da ke yakar Boko Haram

Mon, 14 Mar 2022 Source: BBC

Rundunar sojin Najeriya ta ce nan gaba ne za ta miƙa wasu tsoffin 'yan Boko Haram sama da 500 da ta yaye, hannun hukumomin farar hula, bayan kammala horon raba su da tsauraran ra'ayi.

Ɗaruruwan tsoffin 'yan Boko Haram ne suka yi rantsuwa a ƙarshen mako, tare da kai caffarsu ga gwamnatin Najeriya, da suka yaƙa a baya.

Gwamnatin Najeriya ce ta ɓullo da shirin wanda sojoji ke gudanarwa a 2015, a wani ɓangare na dabarun yaƙi da ta'addanci.

'Yan Boko Haram waɗanda bisa raɗin kansu suka ajiye makamai kuma suka miƙa wuya ga hukumomin ƙasar ne ke cin gajiyar wannan shiri na musamman ciki har da samun horo kan sana'o'in hannu da sauya musu fahimta kan addini.

An ba su tallafin kyautata tunani da nufin sauke su daga tsattsauran ra'ayi, kafin a mayar da su cikin al'umma.

Babban jami'in kula da shirin mai taken 'Operation Safe Corridor', Birgediya Janar Joseph Maina ya ce tun bayan fara gudanar da shi, tsoffin 'yan Boko Haram 1,070 ne tuni aka mayar cikin jama'a.

Da waɗannan tsoffin 'yan Boko Haram da aka yaye a ƙarshen mako adadin waɗanda suka ci gajiyar horon ya ƙaru zuwa mutum 1,629.

Sai dai har yanzu akwai ɗari-ɗari daga ɓangaren al'umma ga tsoffin 'yan Boko Haram ɗin, bisa la'akari da irin taɓargazar da ƙungiyarsu ta tafka.

Hukumomin Najeriya sun ce dubban 'yan Boko Haram ne da iyalansu suka miƙa wuya tun bayan ɓullo da shirin.

Ana aiwatar da shi ne daidai lokacin da hare-haren sojoji ke ci gaba a kan 'yan ta-da-ƙayar-bayan da ke ci gaba da ta'annati a yankunan arewa maso gabas a Najeriya.

Rikicin ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram da aka fara a 2009 ya haddasa mutuwar kimanin mutum dubu 350, ya kuma raba wasu miliyoyi da gidajensu a Najeriya da sauran ƙasashen yankin Tafkin Chadi.

Cikin waɗanda suka samu horon har da tsoffin mayaƙan Boko Haram na wasu ƙasashen Tafkin Chadi.

An yi bikin yaye su ne a Cibiyar raba mutanen da tsattsaurar aƙida da sauya musu hali da kuma mayar da su cikin jama'a.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: