BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Butum-butumin Nasa ya tattaro 'ƙayatattun' samfuran duwatsu a duniyar Mars

Mars Sld Hoton alama

Mon, 19 Sep 2022 Source: BBC

Na'urar Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka mai suna Perseverance ta kusa kammala manufar aikinta ta farko da aka tura ta yi a duniyar Mars.

Butum-butumin ya tattaro mabambantan jerin samfuran duwatsu waɗanda nan gaba kaɗan zai jibge su a can, kafin a kwaso su zuwa duniyarmu ta Earth.

Wata 17 ke nan da butum-butumin ya isa wani yanki da ake kira dandamalin Jezero, wanda ke rataye a jikin sandunan ƙarfen wani kumbo.

Daga abin da butum-butumin wanda kuma ake wa lakabi da Percy ya gani, tuni masana kimiyya suka tabbatar cewa na'urar tana wurin da ya dace don gano ko akwai wata rayuwa a Mars.

Ba wai yana neman wata halitta da ke rayuwa ba ne a yanzu, matsanancin yanayin da duniyar Mars ke da shi, ya sa samun hakan zai yi matuƙar wuya.

Maimakon haka, butum-butumin yana neman ɓurɓushin wata halittar da mai yiwuwa ta wanzu biliyoyin shekaru da suka wuce lokacin da Jezero ya cika da ruwan tafki.

Wannan daɗaɗɗen tarihin, masana kimiyya suna fatan a yanzu yana nan damɓare kan ƙayatattun samfuran duwatsun da za a ajiye a "wani defo" nan da 'yan watanni masu zuwa.

"Idan yanayin tarihin Jezero ya kasance tun da daɗewa a ko'ina ne cikin duniyar Earth a kowanne irin yanayi tsawon sama da shekara biliyan uku da rabi, ina jin akwai tabbaci ko kuma a ƙalla a ɗauka cewa rayuwa za ta iya faruwa kuma ta bar alamominta a kan waɗannan duwatsu don mu masu nazari," in ji David Shuster wani masanin kimiyya daga Jami'ar California a Berkeley da ke bibiyar na'urar Perseverance.

Nasa da Hukumar kula da Sararin Samaniyar Turai na aiki kuma a kan wani shiri don gano ɓaraguzan dutse.

Wannan shi ma wani gagarumin shiri ne da ke ƙoƙarin sake aika na'urori kamar helikwaftoci da wani kumbo mai suna Martian da wani makeken jirgin jigila tsakanin duniyoyi.

Burin, shi ne a kwaso samfuran da aka samu zuwa duniyar az (earth) nan da 2033.

Abubuwan da za a kawo za su haɗar da duwatsun wuta da na'urar Perseverance ta haƙo zuwa saman fafakeken rami.

Waɗannan ne za su fayyace wani labari akasari na yankin Jezero kafin ya cika da ruwan tafki. Muhimmin abu, shi ne samfuran wani nau'in dutse ne da tabbas za a iya sanin shekarunsa.

A yanzu haka, shekaru a duniyar Mars sai dai kawai a yi kintace.

Sauran abubuwan da za a kwaso sun ƙunshi nau'in duwatsun ƙasa da Perseverance ya tattaro a watannin baya-bayan nan daga

diddigar da aka gano a ƙasan marabar ruwan da ke sashen yamma daga faɗin kilomita 45 na fafakeken ramin.

Marabar kogi wata siga ce da ake samu daga rairayi da yashin da ruwa ya jibge a wani wuri lokacin da yake rage gudu kafin ya faɗa cikin wani babban ruwa.

Sigar ta siffofin ƙasa da mai yiwuwa ƙananan halittu suka tattara ta faru ne shekaru aru-aru da suka wuce.

Daya daga cikin samfuran duwatsun, mai laƙabin "Wildcat Ridge" ya taru ne a tafkin Jezero daidai lokacin da taɓo yake bushewa.

Yana cike da sinadaran gishiri. Sai dai na'urorin jikin butum-butumin sun nuna cewa saman dutsen Wildcat yana kuma ƙunshe da ɗumbin ma'adanai na diddigar halittu da sauran sinadaran kabon.

Wannan wani muhimmin abu ne da aka lura da shi, ko da yake yana da gagarumin aibu.

"Duk rayuwa kamar yadda muka sani ta fara ne daga diddigar halittun da suka shuɗe.

Sai dai wani muhimmin abu shi ne diddigar halittu na samuwa ne daga sarrafuwar sinadarai da kuma wasu al'amura da ba su da alaƙa da rayuwa; misali, ta hanyar alaƙoƙin ruwa da duwatsu.

Akwai kuma diddigar halittun da ita ma ake samu daga ƙurar da ta taru a tsakanin taurari," a cewar Sunan da Sharma wata masaniyar kimiyya da ke nazarin wannan aiki a wani ɗakin gwaje-gwajen harba kumbuna na hukumar Nasa.

A tsawon wata huɗu da ya wuce, na'urar Perseverance ya riƙa aiki a kan wata gaɓa mai zurfin mita 40 da ke gefen marabar kogi.

Butum-butumin dai nan gaba kaɗan zai tafi zuwa wata mafaɗa da ke kusa da wani shimfiɗaɗɗen yanki na gajeren ramin, inda ake iya zube samfuran dutse a ƙasa.

"Muna nazari kan yiwuwar kawo samfur 10 zuwa 11 nan doron ƙasa", a cewar injiniyan kula da aikin, Rick Welch.

Daga nan za a shafe kimanin wata biyu don mai yiwuwa a ajiye waɗannan samfura kuma cikin tsanaki a taskace bayanan wurin da suke, ta yadda idan an tashi yin wani aiki a gaba, to za a iya samu.

Ranar 19 ga watan Oktoba ne ake sa rai Nasa za ta yanke shwarar ko a ci gaba/ko a bar wannan gagarumin aiki bayan wata ganawa.

Masana kimiyyar na son kwaso ƙarin samfura, kuma aikin kwasowar zai fi mai da hankali ne a kan inda butum-butumin zai je a nan gaba.



Read full article

Source: BBC