BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Chelsea na zawarcin Bellingham, Barcelona ta ce Messi zai dawo

E6a289a0 3f87 11ed 9ae9 959994b8a64c Jude Bellingham

Thu, 29 Sep 2022 Source: BBC

Chelsea ta shiga sahun masu fafutikar sayen ɗan wasan Ingila da Borussia Dortmund da ke buga tsakiya Jude Bellingham – mai shekara 19 kan £130m, Liverpool da Real Madrid duk na zawarcinsa. (Telegraph - subscription required)

Dan wasan gaba a Paris St-Germain Lionel Messi, mai shekara 35, na iya komawa Barcelona a cewar mataimakin shugaban kungiyar Eduard Romenu, wanda ya shaidawa tashar rediyon Sifaniya cewa akwai yiwuwar dawo da ɗan wasan. (The Sun)

Manchester City na shirin shiga tattaunawa da ɗan wasansu na tsakiya asalin Portugal Bernardo Silva domin fahimtar ko zai sauya sheƙa a karshen kaka, sau biyu ɗan wasan mai shekara 28 yana nuna alamomi bankwana da kungiyar. (Mail)

Arsenal har yanzu na zawarcin ɗan wasan nan mai shekara 24 Douglas Luiz daga Aston Villa domin maye gurbinsa da Thomas Partey mai shekara 29 na Ghana da ya samu rauni.

Kocin kungiyar Mikel Arteta ya gaza kawo Luiz kungiyar, amma yana son ya sake gwada sa’arsa a karo na uku kan ɗan wsaan da ke buga tsakiya a Brazil, bayan watsi da tayinsa sau biyu a rana ta karshe na rufe kasuwar cinikin ‘yan kwallo. (The Sun)

Barcelona ta kwaɗaitu da ɗan wasan Manchester City da Jamus da ke buga tsakiya Ilkay Gundogan, shekara guda ya ragewa ɗan wasan mai shekara 31 kwatiraginsa ya kare. (Sport)

Bayanai na cewa Wolves ta saye ɗan wasan Chile mai buga tsakiya Dario Osario dan shekara 18 daga Universidad de Chile kan £5.5m wanda aka rinka alakantawa da Real Madrid da Manchester City. (Express)

Tottenham na son dauko mai tsaron ragar Atletico Madrid da Slovenia Jan Oblak, mai shekara 29, domin maye gurbin Hugo Lloris. (Evening Standard)

Shugaban Paris St-Germain Nasser al-Khelaifi ya ce sayar da kadororinta da Barcelona ta yi domin siyo ‘yan wasa babu adalci a ciki kamata ya yi Uefa ta yi bincike kan halascin yin hakan. (ESPN)

Tottenham na shirin dauko ɗan wasa daga Sweden Dejan Kulusevski, mai shekara 22, idan kwantiraginsa ya kare a Juventus. (Fabrizio Romano)

Atletico Madrid na duba yiwuwar mika tayi kan mai tsaron ragar Manchester United David de Gea mai shekara 31 yayin da kwantiraginsa ke kawo karshe. (90min)

Everton ta shaidawa ɗan wasan Venezuela Salomon Rondon, cewa yana da damar neman wata kungiyar a Janairu, bayan gaza tafiya Turkiyya a wannan watan. (Football Insider)

Dan wasan baya a Portugal Diogo Dalot, mai shekara 23, na fatan samun sabon kwantiragi daga  Manchester United.

Barcelona da Juventus da Atletico Madrid da AC Milan da Roma na sa ido kan Dalot. (Manchester Evening News)

Chelsea na iya sake dawo da ɗan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 24, daga Roma. (Fabrizio Romano)

Christian Pulisic ba ya son bankwana da Chelsea bayan alakanta shi da kungiyoyi da dama, ciki har da Manchester United, a lokacin bazara.

Nada Graham Potter da Chelsea ta yi na nufi ɗan wasan mai shekara 24 na da damar sake gina kansa. (Evening Standard)

Chelsea na son sayo ɗan wasan Slovakia Milan Skriniar daga Inter Milan wanda kwantiraginsa ke karewa a karshen wannan kaka. (Calciomercato - In Italian)



Read full article

Source: BBC