BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Coronavirus: Tanzania ta yi amai ta lashe kan annobar

 119628855 Hi067137150 Samia Suluhu Hassan ce shugaban Tanzania

Thu, 29 Jul 2021 Source: BBC

Shugaba Samia Suluhu ta kasance mutum na farko da aka yi wa allurar rigakafin korona bayan kaddamar da shirin a ƙasar.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen adawa da magabacinta Marigayi Shugaba John Magafuli ya dinga nunawa bayan rashin amincewa da cutar kafin ya rasu sakamakon matsalar zuciya a watan Maris.

Tsohon shugaban bai yarda da ingancin rigakafin ba, kuma Tanzania ba ta shiga gangamin aminta da rigakafin ba.

Me ya sauya ƙarkashin sabuwar shugaban ƙasar?

A bikin ƙaddamar da soma rigakafin, Shugaba Samia ta umarci 'ƴan Tanzania su karɓi allurar, tana mai cewa ƙasar ba "tsibiri ba ne".

A watan Yuni, ta amince ƙungiyoyi da ofisoshin ƙasashen ƙetare su shigar da rigakafin ga ma'aikatunsu d ake ƙasar.

Tanzania ta kuma nemi damar shiga tsarin tallafin annobar korona na duniya wato Covax, kuma ta karɓi rukunin farko samfurin Johnson & Johnson miliyan ɗaya daga Amurka a ranar 24 ga watan Yuli.

Yankin tsibirin ƙasar da ba shi da cikakken 'yanci na Zanzibar ya soma bayar da rigakafin samfurin Sinovac wanda China ke samarwa mako biyu da suka wuce.

Tarayyar Afirka ta kuma ce Tanzania ta shiga shirinta na sayen rigakafi.

A watan Mayu, Shugaba Samia ta nuna shakkunta a kan rigakafin annobar, lokacin da ta shaida wa al'ummar Musulmi cewa ta fahimci damuwar da suke nuna wa kan rigakafin kuma gwamnatin ta "ba za ta aminta da abin da aka kawo musu ba ko aka ce su yi amfani da shi".

"Ko a kan batun rigakafin, sai mun gamsar da kan mu kafin yanke hukunci kan amfani da shi ko akasin haka," a cewarta.

Mutane da dama musamman magoya bayan tsohon shugaban ƙasar na ci gaba da nuna adawarsu da rigakafin.

Misali, akwai wani malamin coci, Joseph Gwajima, wanda mamba ne a majalisa da ke ikirarin cewa rigakafin na iya birkita kwayar halitta ta DNA, ba tare da ya bayar da wata shaida ba.

Me sabuwar shugabar tace akan cutar korona?

Ta amince da cewa annobar na yaɗuwa tare da bukatar mutane su yi taka-tsan-tsan:

  • wanke hannu


  • sanya takunkumi


  • bai wa juna tazara


  • A watan Yunin 2020, bayan fama da barkewar annobar karo na farko, Shugaba Magafuli ya sanar da cewa babu annobar a ƙasarsa, kuma tun da farko bai karfafa gwiwa kan amfani da takunkumi ko nuna alamomin Tanzania za ta bukaci rigakafi ba.

    "Na yarda cewa... Ubangiji ya kawo karshen annobar korona," a cewarsa.

    Shugaba Magufuli ya karfafa gwiwar a dinga:

  • Sallah


  • motsa jiki
  • sirace


  • shan maganin gargajiya


  • Game da batun sirace da sauran magunguna, Shugaba Samia na da ra'ayi guda a kan wannan fatawar.

    Tana mai cewa:

  • kar mutane su sare a kan batun sirace kuma ta karanta cewa yana taimakawa a matakin farko na kamuwa da cuta


  • ba kuma daidai ba ne a yi watsi ko yasar da magungunan gargajiya


  • "Idan kana ganin sirace na taimakawa, ka je ka yi," a cewar Shugaba Samia.

    "Idan kana ganin shan wani magani zai taimaka, ka sha abinka."

    Sai dai babu shaida da ke nuna sirace na taimakawa wajen magani annobar korona.

    Shugaban likitoci a Tanzania, Shadrack Mwaibambe, ya ce gwamnati ta dakatar da wannan maganar, saboda a kimiyyance babu wannan batu.

    Wane mataki sabuwar shugabar ta ɗauka?

    Lokacin da ta hau mulki, Shugaba Samia ta kafa kwamitin kar-ta-kwana kan korona.

    A tsakiyar watan Mayu, ta bayar da wadannan shawarwari:

  • tabbatar da al'umma su amince da annobar


  • a dinga sanar da mutane yadda alkaluman suke a hukumance


  • Tanzania ta shiga shirin tallafin annobar korona na duniya Covax


  • A farkon kwanakin mulkinta, Shugaba Samia ta sha bayyana a bainar jama'a ba tare da sanya takunkumi ba.

    Amma takan sa takunkumi idan za ta kai ziyara ƙetare (Uganda da Kenya) kuma a yanzu takan ɗan saka a Tanzania.

    Ma'aikatun gwamnati na ta kira ga mutane su dinga sanya takunkumi.

    Akwai kuma sabbin sharuɗa kan sake buɗe makarantu, ciki har da:

  • sanya takunkumi


  • bai wa juna tazara
  • tabbatar da wanke hannu da amfani da sinadarin tsaftace hannu


  • Ya ake ciki kan batun alkaluman annobar a hukumance?

    Lokacin da annobar ta soma a 2020, Tanzania kan wallafa alkaluman masu kamuwa da kuma mutuwa - amma daga baya suka dakatar.

    A yanzu gwamnatin na wallafa alkaluman, sai dai ba kullum ba kamar yadda ake gani a sauran kasashe.

    Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce daga yanzu za ta ke sanar da alkalumanta bayan kowanne mako biyu.

    A watan Yuni, a wani taro a Dar es Salaam, Shugaba Samia ta sanar da cewa: "Muna da mutane sama da 100 dauke da cutar, cikinsu mutum 70 na samun taimakon numfashi daga na'ura, sauran kuma na shan magani," a cewarta.

    A ranar 21 ga watan Yuli, ma'aikatar ta ce akwai mutum 682 ɗauke da cutar kwance a asibiti a sassan ƙasar, 29 daga cikinsu sun mutu.



    Read full article
    Source: BBC