BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Cristiano Ronaldo: Likitoci sun kammala auna koshin dan kwallon Portugal

 120334250 Gettyimages 1325096632 Cristiano Ronaldo

Mon, 30 Aug 2021 Source: BBC

An kammala auna koshin lafiyar Cristiano Ronaldo a Manchester United a karshen mako a shirin da yake na komawa kungiyar daga Juventus.

Sky Sports ya bayar da rahoton cewar tuni kyaftin din tawagar Portgal ya amince da yarjejeniyar kaka biyu ranar Litinin.

A makon jiya United ta sanar da cewar ta kulla yarjejeniyar sake daukar Ronaldo daga Juventus, bayan da dan kwallon ya nemi izinin barin kungiyar Italiya.

Har yanzu United ba ta fayyace kunshin cinikin ba, ana kuma sa ran rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a Premier ranar Talata da dare.

Sky Sports ya bayar da rahoton cewar kudin da United ta dauki dan kwallon zai kai Yuro miliyan 15 da karin tsarabe-tsarabe da ya kai Yuro miliyan takwas.

Ana sa ran Ronaldo zai fara buga wa United kwallo a karawar da za ta yi da Newcastle United a Old Trafford ranar 11 ga watan Satumba.

Ronaldo ya ci kofi takwas a United tsakanin 2003 zuwa 2009 da Ballon d'Or da kyautar fitatcen dan wasa a 2008

Daga nan ne ya koma Real Madrid kan wanda aka saya mafi tsada a duniya kan fam miliyan 80.



Read full article

Source: BBC