BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Cryptocurrency: Mutanen da aka talauta ta hanyar sace musu kuɗaɗen Bitcoin

 120242342 Tidypicture Mutane da dama sun yi rashin dukiya sabo da tallar Bitcoin

Sun, 29 Aug 2021 Source: BBC

Wani direban tasi mai suna Chris yana yawan duba wayarsa don ganin sabbin bayanai.

"Na kusa yin asarar kusan euro 2,500 na kuɗaɗen intanet na crypto," a cewarsa.

Chris ya bayyana kansa a matsayin "wani mamallakin kuɗaɗen crypto ne daga Austria" kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da aka yi wa kutse ta intanet don sace musu kuɗaɗen cyrpto na kamfanin Liquid Global a makon da ya wuce.

Kamfanin ya dage cewa zai biya dukkan abokan hulɗarsa da suka yi asara a kutsen da aka sace dala miliyan 100.

Amma abokan hulɗa da dama sun shiga cikin damuwa kafin a mayar musu da kuɗaɗen nasu.

Kowane lokaci Chris mai shekara 38 ya ɗauki fasinja a wata tsohuwar motarsa ƙirar Volkswagen, sai ya ta da batun halin da yake ciki.

"Motata ta tsufa don ta fi shekara 20, kuma da a ce ba a min kutsen nan ba da na sayi sabuwa da kuɗin," a cewar Chris.

"Ba zan iya cewa bala'i ne ba, amma gaskiya lamarin babba ne a gare ni. Ina buƙatar a ƙalla shekara ɗaya kafin na sake tare irin wannan kuɗin."

'Damuwata ta kai kashi takwas cikin 10'

A Indonesia, Dina mai shekara 27 ta ce ta kaɗu matauƙa. "Ina matuƙar jin haushin masu kutsen, kuma ina cikin matuƙar damuwa.

"Ina da kusan dala 30,000 kuma ina buƙatar kuɗaɗen nan don al'amuran yau da kullum. Ni matar aure ce da nake ƙoƙarin samun kuɗi ta hanyar crypto."

Shi kuwa wani likita ɗan ƙasar Norway mai shekara 42, ya ce yana ta ƙoƙarin samun nutseuwa, saboda zai iya rasa arziƙin da ya yi ta fafutukar tarawa cikin tsawon shekaru.

"Jumullar abin da nake da shi a kamfanin Liquid ya kai euro 969,000. Gaskiya abin na matuƙar damuna kuma damuwar tawa ta kai kashi takwas cikin 10. Ko yaushe tunanin lamarin nake yi."

Iyayen da ke cikin fargaba

A Sydney, James ya bayyana damuwar da masu kutse suka sanya iyayensa a ciki, waɗanda suka samu sukunin cire kuɗaɗen kafin kamfanin ya toshe shiga da fitar kuɗaɗe.

"Mahaifiyata da mahaifina suna da kuɗin Bitcoin ɗaya a ciki, wanda kuɗinsa ya kai kusan dalar Australiya 37,000. Wannan kudi ne mai matuƙar yawa da muhimmanci a gare su.

"Gaskiya akwai ɗaga hankali. Da farko ba su fahimci me ke faruwa ba, daga baya suka gane cewa an tilasta musu cirewa ne da kuma sayar da shi a cikin fargaba, wanda hakan ke nufin sun yi asarar kusan dala 10,000.

A makon da ya gabata ne aka yi wa kamfanin Liquid Global kutse, sai dai akwai yiwuwar za su iya samun kuɗaɗensu.

Kamfanin wanda ke ƙasar Japan a ranar Laraba ya ce, zai yi wani duba na tsanaki kan sha'anin tsaronsa yana kuma son tabbatar wa masu amfani da shi cewa ba za su sake fuskantar matsala irin wannan ba.

Abokan hulɗa da dama sun yi ƙorafi cewa ba a gaya musu komai game da batun kutsen ba kai tsaye, kuma da ba za su san komai kan hakan ba ba don sun ga saƙon da kamfanin ya wallafa a Tuwita ba.

Ko amfani da kuɗaɗen ba ya tattare da matsala?

Musayar kuɗaɗe kamar na kamfanin Liquid abu ne mai muhimmanci na haɓakar kasuwar cryptocurrency.

Shafin intanet dinsu na ba da damar saye da sayar da kuɗaɗen intanet irin su Bitcoin da Ethereum, sannan waje ne da mutane ke iya ajiye kuɗaɗensu na intanet cikin aminci.

Sai dai duk da haka akwai ayar tambaya kan tsaron musayar kuɗaɗen.

A farkon watan nan, an yi kutse a wani shafin na hada-hadar crypto da ake kira Poly Network, sannan ya yi asarar dala miliyan 610 na kuɗaɗen abokan hulɗarsa.

An sace a ƙalla fan biliyan 1.6 tun daga shekarar 2014 a shafukan intanet na hada-hadar crypto a faɗin duniya.

Gagaruman kutsen da aka yi

  • BitGrail: an yi wa kamfanin na Italiya kutse aka sace dala miliyan 146 a 2018. An ƙiyasta cewa masu amfani da BitGrail 230,000 ne suka yi asarar kuɗaɗensu.


  • KuCoin: an sace dala miliyan 281 da ake zargin wasu ƴan Koriya Ta Arewa ne suka yi kutse suka sace daga shafin wani kamfani da ke Seychelles a 2020. Daga baya kamfanin ya ƙwato kuɗaɗen da dama ya mayar wa abokan hulɗa.
  • MtGox: an sace dala miliyan 450 na bitcoin a 2014 wanda sanadin haka kamfanin ya durƙushe. Har yanzu ba a mayarwa abokan hulɗa kuɗaɗensu ba.


  • Coincheck: an sace dala miliyan 534 a 2018 daga kamfanin na Japan. Daga baya an mayar wa abokan hulɗa kuɗaɗensu.


  • Poly Network: an sace dala miliyan 610 daga wani shafin China a farkon watan nan. Wanda ya yi kutsen ya mayar da dukkan kuɗaɗen sannan an fara mayar wa abokan hulɗa abinsu.


  • Kusan duk wata ana samun irin wannan kutse na miliyoyin daloli a shafukan da yawanci ba a saka musu ido, babu tabbas ko abokan hulɗa na iya samun kuɗaɗensu.



    Read full article
    Source: BBC