BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Dakarun Tigray sun karɓe iko daga gwamnatin Habasha

Tigray Armoured Car Dakarun Tigray wato TDF sun ce suke mallakar baban birnin Tigray wato Mekelle

Tue, 29 Jun 2021 Source: BBC

Gwamnatin Habasha ta sanar da zagaita wuta a yankin Tigray wata takwas bayan firaminista Abiy Ahmed ya tura dakaru su tumbuke jagororin gwamnatin yankin.

Sanarwar tsagaita wutar ta zo ne yayin da shaidu a yankin ke cewa dakarun da ke yakar gwamnatin tarayyara kasar sun shiga Mekelle, babban birnin yankin Tigray.

Ana tuhumar dukkan bangarorin biyu da aikata laifukan yaki kamar kisan kiyashi da take hakkin dan Adam.

Fiye da mutum miliyan biyar na cikin wani mawuyacin halin rashin abinci, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, tana cewa mutum 350,000 na fuskantar yunwa.

Sai dai bayanan da ke fitowa daga yankin ranar Litinin na cewa mayakan Tigray - wadanda a makon jiya su ka kai wani farmaki - sun kori gwmnatin rikon kwarya daga Mekelle.

Gatachew Reda, wanda shi ne kakakin dakarun Tigray People's Liberation Front (TPLF), ya sanar da Reuters cewa birnin ya koma karkashin ikon su a halin da ake ciki.

Wasu mutane a Mekelle sun fara murnar ficewar dakarun gwamnatin tarayyar kasar, kuma wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "kowa ya fice", inda wani kuma ya shaida wa Reuters cewa ya ga sojojin Tigray a Mekelle.

Kawo yanzu dai babu abin da gwamnatin ta Habasha ta ce kan rahotannin ficewar dakarun na ta.



Read full article

Source: BBC