BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

EFCC ba ta kama ni ba- Al-Makura

 119642119 Tankoalmakura Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura

Thu, 29 Jul 2021 Source: BBC

Latsa hoton da ke sama don saurarar hirar da muka yi da Sanata Al-Makura



Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa jami'an hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa, wato EFCC sun kama shi tare da iyalinsa.

Jaridar Premium Times a Najeriya ce ta ruwaito labarin kama Sanata Al-Makura ranar Laraba, inda ta ce EFCC ta tsare tsohon gwamnan da mai ɗakinsa bisa zargin almundahana.

Amma Al-Makura, wanda a yanzu shi ne Sanata da ke wakiltar Nasarawa ta kudu a majalisar dattawan Najeriya ya tabbatar da cewa hukumar ta gayyace shi game da wadansu korafe-korafe da aka yi a kansa ne, kuma da kansa ya je hukumar inda ya gana da shugabanta da wasu jami'ai, ganawar da ba ta wuce wani gajeren lokaci ba.

Ya zargi masu yada jita-jitar an kama shi da cewa suna so ne su shafa masa kashin kaza ko bata masa suna, amma ba su yi nasara ba.

"Wannan jita-jita ta ba ni mamaki, ta ba mutane da dama mamaki," a cewar Sanata Al-Makura.

Ya ce dama hukumar EFCC ta gayyace shi tun kafin Sallah amma ya shaida masu cewa ba zai samu damar amsa gayyatar ba sai bayan Sallah, shi ya sa kuma ya shirya ya je don jin dalilin gayyatar.

Sanata Al-Makura ya ce "Ko da na je na gana da shugaban hukumar, sai ya sanar da ni cewa dama korafe-korafe ne da mutane ke yi a kaina, kuma ana son a ji ta bakina. Ganawata da shugaban EFCC duka ba ta wuce minti goma ba."

Haka kuma, ya ce ya tattauna da wasu jami'an hukumar kan korafe-korafen da aka shigar a kansa kuma ya bayar da amsa gwargwadon saninsa.

Sanatan mai wakiltar Nasarawa ta Kudu ya musanta zargin da wasu ke yi na cewa gayyatar da EFCC ta yi masa na da nasaba da takarar shugabancin jam'iyyar APC da ya ke yi.

"Masu wannan maganar na yi ne don daƙushe neman kujerar shugabancin APC na ƙasa da mutane da dama ke so in yi. Sai dai ni ba ni da damuwa da kowa," a cewarsa.

Ya ce mai yiwuwa akwai masu wata manufa a gare shi sabanin wanda masoyansa ke da shi a kansa.

Sanata Al-Makura ya ce shi ɗan Najeriya ne mai bin dokar jam'iyya, shi ya sa ma bai zage wajen yin kamfe din shugabancin jam'iyyar APC ba.

"Na tsaya ne saboda a matsayina na dan jam'iyya mai bin umarnin shugabannin jam'iyya, na jira ne in ji irin ka'idojin da za su sa da inda jam'iyyar ta dosa kafin in bude fagen neman shugabancin jam'iyyar," a cewarsa.



Read full article

Source: BBC