BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Eder Militao zai yi jinya mai tsawo a Real Madrid kamar Courtois

8868a6a0 39f3 11ee Bde6 7ffba94c56ae Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya ji rauni a gasar Madrid da Athletic Bilbao

Mon, 14 Aug 2023 Source: BBC

Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya ji rauni ranar Asabar a wasan farko a La Liga da Real Madrid ta ci Athletic Bilbao 2-0.

Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 25, shi ne na biyu a Real Madrid da ya ji rauni bayan Thibaut Courtois ke jinya tun daga ranar Alhamis.

An sauya Militao a karawar ta La Liga, bayan raunin da ya ji a gwiwar kafarsa.

Real Madrid ta sanar cewar likitoci za su yi wa dan kwallon tiyata, daga nan za a fayyace ranar da zai koma taka leda.

Sabon dan wasan da Real ta dauka a bana, Jude Bellingham ne ya fara ci mata kwallon farko ranar Asabar, wanda ta dauka daga Borussia Dortmund.

Raunin da Militao ya ji, ya bar koci, Carlo Ancelotti da masu tsaron baya daga tsakiya masu lafiya da suka hada da David Alaba da Antonio Rudiger da kuma Nacho.



Read full article

Source: BBC