BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Enyimba 2-1 Rangers: Kungiyar Aba ta doke Rangers a wasan hamayya

 124109996 Mediaitem124109995 Yan wasan Firimiya na Najeriya | Hoton alama

Mon, 11 Apr 2022 Source: BBC

Enyimba ta yi nasara a kan Enugu Rangers da ci 2-1 a gasar Firimiyar Najeriya da suka kara ranar Lahadi.

A wasan na hamayya Rangers ce ta fara cin kwallo ta hannun Martin Ossy a minti na 15 da fara tamaula, daga baya Victor Mbaoma ya farke kan hutu.

Enyimba ta ci na biyu ta hannun Victor Mbaoma kuma na biyu da ya zura a raga a jarawar.

A wasan farko da suka hadu a bana Enyimba ta yi nasara, kenan a karon farko ta doke Rangers gida da waje tun bayan sama da shekara 20.

Sakamakon wasannin mako na 22 da aka buga ranar Lahadi:

  • Lobi 0-0 Kano Pillars
  • Enyimba 2-1 Enugu Rangers


  • Sunshine 1-0 Abia Warriors


  • Niger Tornadoes 1-0 Wikki Tourist


  • MFF 2-0 Dakkada


  • Wasannin mako na 22 da za a buga ranar Litinin:

  • Gombe United da Nasarawa United


  • Akwa United da Shooting Stars


  • Kada City da Plateau United




  • Read full article
    Source: BBC