BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Euro 2020: Switzerland ta fitar da France daga gasar nahiyar Turai

 119127605 Kylianmbappefrance2 Kyliam Mbappe, dan wasan PSG da tawaggar Faransa

Tue, 29 Jun 2021 Source: BBC

Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta yi ban kwana da gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da Switzerland ta yi waje da ita a bugun fenariti da ci 5-4.

Tun farko tawagogin biyu sun tashi wasa 3-3, hakan ya sa aka yi karin lokaci nan ma ba a fidda gwani ba a wasan zagaye na biyu a gasar ta cin kofin Turai ta bana.

Hakan ne ya sa aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda Switzerland ta ci dukkan kwallo biyar din da ta buga.

Tawagar Spain ta kai quarter final a Euro 2020 Ita kuwa Faransa mai rike da kofin duniya ta ci hudu, kuma Kylian Mbappe ne na biyar da idan ya ci a kara kiran wasu 'yan wasan don ci gaba da bugun fenariti.

Sai dai yana buga kwallon golan Switzerland, Yann Sommer ya tare, wanda da farko ya dauka alkalin wasa dan Argentina zai ce ya bar layi a sake bugun fenaritin, amma sai yaga an tashi daga wasan.

Wannan shi ne karon farko da Switzerland ta kai quarter finals a babbar gasar tamaula a duniya tun bayan 1938.

Switzerland za ta buga daf da na kusa da na karshe da Sifaniya ranar Juma'a a St Petersburg, bayan da Sifaniya ta doke Croatia da ci 5-3 a ranar Litinin.



Read full article

Source: BBC