BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Fikayo Tamori ya koma AC Milan daga Chelsea kan £24m

 118762842 Gettyimages 1232646168 Fikayo Tomori

Fri, 18 Jun 2021 Source: BBC

Kungiyar AC Milan ta dauki mai tsaron bayan Chelsea, Fikayo Tomori kan fam miliyan 24, bayan da ya taka rawar gani a wasannin aro da ya buga a Italiya a kakar da ta kare.

Ya koma Italiya da murza leda bayan da AC Milan ta cika yarjejeniyar mallakar dan wasan, wanda ya koma kungiyar a watan Janairu daga Chelsea.

Mai shekara 23, mai tsaron bayan tawagar Ingila ya saka hannu kan kwantiragin kaka hudu a kungiyar da ke buga gasar Serie A.

Tomori ya buga wa Milan wasa 22 da cin kwallo daya a kakar da aka kammala.

Wanda ya fara Chelsea tun daga makarantar kungiyar ya kasa samun gurbin taka leda a karkashin koci Frank Lampard a bara, duk da taka rawar gani da ya yi a kakar 2019-20



Read full article

Source: BBC