Dan wasan tawagar Sifaniya, Gavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a Barcelona zuwa karshen kakar 2026.
Tuni Barca ta gindaya £865m ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan idan kwantiraginsa bai kare ba a Camp Nou.
Mai shekara 18 ya fara yi wa Barcelona tamaula tun daga 2015, wanda yake da yarjejeniyar da za ta karkare a karshen 2023 tun farko.
Ya fara buga wa kungiyar tamaula a Agustan 2021 yana da shekara 17 da kwana 24, shi ne matashi na hudu da ya fara yi wa kungiyar wasa a tarihi.
Gavi ya buga dukkan wasannin da Barcelona ta fafata a La Liga a kakar nan.
Ya zama matashi na uku a Barcelona da ya ci kwallo, wanda ya yi wannan bajintar a karawa da Elche a Disambar 2021.
Tsohon matashin tawagar Sifaniya, wadda ya fara yi mata tamaula a Oktoban 2021, ya zama matashin da ya wakilci kasar a tarihi.
Gavi ya zama matashin Sifaniya da ya ci mata kwallo a karawa da Jamhuriyar Czech a watan Yuni.
Lokacin yana da shekara 17 da kwana 304 - ya doke tarihin da Ansu Fati na Barcelona ya kafa a 2020.
Read full article