BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Google ya cika shekara 23: Ga abubuwa 21 da ba ku sani ba game da Google

Google Phone Google ne shafin da aka fi ziyarta a duniya

Tue, 28 Sep 2021 Source: BBC

An fara wallafa wannan makala a ranar 27 ga watan Satumban 2019 lokacin da shafin ya cika shekara 21. Mun sabunta shi a yanzu da ya cika shekara 23 da budewa.

Google ya cika shekara 21 a ranar Juma'a 27 ga watan Satumba! Mutane da dama ne daga kowane sassa na duniya ke amfani da fitaccen shafin na matambayi ba ya bata, kuma yana da muhimmanci sosai ga dumbin jama'a.

Domin bikin wannan rana, mun tattaro wasu bayanai na hakika daga kamfanin wadanda ba lallai ku sani ba - sai dai idan kun tambaya a shafin google din.

1. Abin da zai ba ku mamaki shi ne cewa Google ne shafin da aka fi ziyarta a duniya - ko a takwaransa shafin Bing ma Google din ne abin da aka fi dubawa.

2. Wasu daliban kwaleji biyu ne suka kirkiri shafin Google masu suna Larry Page da Sergey Brin. Sun so su kirkiri wani shafin intanet ne wanda zai jero shafuka kan yadda wasu shafukan ke alakanta kansu da su, da zai dan yi kama da shafin intanet.

3. Kalmar Google ta samo asali ne daga 'googol', wacce ita ce ta farko da ta biyo bayan sifili 100. Wadanda suka kirkiri shafin sun zabe ta ne don ta dinga nuna bayanai masu dumbin yawa da suke nema ta hanyarta.

4. Shafin 'google doodle' wanda shi ne irinsa na farko (a lokacin da Google ya sauya bangon shafinsa domin shaida wani abu mai muhimmanci) an kirkire shi ne a lokacin bikin 'Burning Man Festival' na shekarar 1998. Wadanda suka samar da shafin na so mutane sun san dalilin daya sa suka fice daga ofishin.

5. Wasu daga cikin abubuwan da Google suke tunawa shi ne bikin gano ruwa a duniyar wata da kuma ranar bikin haihuwar John Lennon na cika shekara 70, wanda shi ne bidiyon farko irin shi a doodle.

6. An ajiye ma'adanar bayanan intanet ta farko da Google ya mallaka ne a wani akwati da aka hada da robobin Lego..

7. Ana kiran shelkwatar Google da 'Googleplex' wanda ke a Silicon Valley da ke California.

8. A Googleplex din, akwai wani katon gunkin dabbar Dinosaur, wanda yawanci yake kewaye da balbelu. Ana rade-radin cewa hakan na tunatar da ma'aikatan Google din kar su bari a manta da kamfanin ko ya zama tarihin kamfanin ya shafe.

9. Shelkwatar katafariya ce kuma akwai itace da ciyayi da yawa. To a maimakon a yi amfani da nau'rar yanke ciyawa, Google na hayar awaki ne domin yanke musu ciyayi.

10. Google ne babban kamfanin fasaha na farko da ya fara bai wa ma'aikatan shi abinci kyauta su kuma bari ma'aikatansu su zo da karnukansu wurin aiki.

11. An kaddamar da shafin duba hoto na Google a watan Yulin shekarar 2001 kuma koriyar rigar da kamfanin Versace ya yi wanda Jennifer Lopez ta sanya a karbar lambobin yabo na Grammy ne ya zaburara da samar da shafin. Rigar ce ta zama abin da aka fi dubawa a shafin, sai a zahiri baza'a iya ganin sa ba.

12. Google ya fara sanar da ayyukansa na e-mail wadanda aka fi sani da G-mail a ranar 1 ga watan Afrilu wato (April Fool's Day) na shekarar 2004. Ganin haka, sai mutane ba su dauka cewar da gaske ba ne.

13. An kara kalmar 'google' a kamus din Merriam-Webster a shekarar 2006, wanda ke bayanin ma'anar kalmar da cewar ayi amfani da shafin domin samun bayanai akan adireshin intanet a na duniya wato World Wide Web.''

14. Youtube ya zama cikin daya daga cikin manhajojin Google a 2006, bayan an sayar da shi fiye da dala biliyan daya da dubu 500. A yanzu haka, shafin YouTube na da masu amfani da shafin kusan mutum biliyan biyu a kowane wata, ana kuma shafe fiye da awanni 400 ana sauke bidiyo a kowane minti.

15. Wani marubucin manhajar kwamfiyuta a Google ya yamutsa hazo a intanet bayan da ya kara '/' bisa kuskure ga rajistar shafin kamfanin. Sakamakon haka, a kusan ko wanne shafin intanet aka samu '/', lamarin da ya sa aka kasa samun komai a intanet din.

16. Kashi 15% cikin 100 na binciken bayanai da ake yi a kullum a Google ba a taba bincike a kansu ba.

17. A watan Afrilun 2018 ne Google ya zama kamfani na farko da ya cimma kashi 100 bisa 100 na samun makamashi maras gurbata muhalli. Wannan na nufin kamfanin na da damar sayen kilowatt na makamashin da zai yi amfani da shi a duk kilowatt daya da ya yi amfani da shi.

18. Hasali Google na da akalla bukukuwan ranar haihuwa guda shida, sai dai ya zabi ya yi murnar bikin a ranar 27 ga watan Satumba.

19. Google na da dabaru da dama wajen bincike. Misali, idan kana neman ma'anar kalmar 'askew', to duka amsoshin da zai baka za su zo a murde.

20. Ga duk binciken da aka gudanar a shafin Google, ana bukatar daukacin fasahar kwamfiyutar da aka yi amfani da ita don aikawa ga 'yan sama jannatin Kumbo Apollo 11 a duniyar wata.

21. A zamanin yanzu, Google ya zarce injin din nema ko tattara bayanai kawai, a nan gaba ana shirin kara abubuwa kamar su basirar na'urori, da sabon wasanni na intanet har ma da motocin da basu da matuka.



Read full article

Source: BBC