BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Hare-haren 'yan bindiga a Jihar Filato sun raba mutum 4,000 da muhallansu

 124170809 7225d0c6 A7b9 4952 B6bb 285d52e2c2e1 Yan bindiga sun addabe yan Najeriya musamma a arewacin kasa

Sat, 16 Apr 2022 Source: BBC

Hukumomi a Najeriya sun ce mutum fiye da 4,000 ne aka raba da muhallansu sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai kan ƙauyuka huɗu a Jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar.

'Yan bindigar sun afka wa ƙauyukan na Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura ranar Lahadi da ta gabata, inda suka kashe mutum aƙalla 150 da kuma ƙona ɗumbin gidaje, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC Hausa.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanam/Kanke, Yusuf Adamu Gagdi, ya faɗa wa BBC Hausa cewa akasarin 'yan gudun hijirar mata ne da yara da suka tsere zuwa maƙotan ƙauyuka.

"Suna cikin tashin hankali," in ji shi. "Na nemi a tura ƙarin jami'an tsaro yankin don a zaƙulo 'yan bindigar nan daga dazukan da suke sannan a kafa sansanin jami'an tsaro a wurin don kare haƙƙin al'umma."

Wasu daga cikin mutanen daga ƙauyukan Kukawa, da Gyambau, da Kyaram, da Dungur na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira, yayin da wasu ke zaune a gidajen mazauna yankunan.

Kazalika, wasu sun tsallaka maƙwabtan jihohi kamar Bauchi.

A ranar Litinin ma 'yan bindiga sun kashe kusan mutum 25 a Jihar Benue mai maƙwabtaka da Filato.

A ranar Talata, Majalisar Wakilai ta buƙaci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tura ƙarin jami'an tsaro da kuma kafa sansanonin soja na dindindin a yankin.

'Na san mutum fiye da 50 daga cikin waɗanda aka kashe'

Latsa hoton da ke sama ku saurari hira da ɗan majalisa Yusuf Adamu Gagdi



Dan Majalisar Wakilai Yusuf Gagdi wanda shi ne shugaban kwamatin sojan ruwa na Najeriya, ya ce mutum kusan 50 na waɗanda aka kashe sun san shi ya san su.

"Zan iya faɗa maka sunan mutum 50 daga cikinsu, babu wanda abin ya fi shafa sama da ni," a cewarsa.

"A cikinsu, akwai mutum 19 da suka yi mani jami'an shirya kamfe lokacin da nake neman zama ɗan majalisar jiha a 2015. A 2019, mutum 24 da aka kashe su ne shugabannin zaɓe na na wannan yankin."

Ya kamata Buhari ya sauka daga mulki saboda ba zai iya magance matsalar tsaro ba - Ƙungiyar Dattawan Arewa

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NbEF) ta nemi Shugban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki nan take sakamakon kashe-kashen da ake fama da su a faɗin ƙasar, musamman a arewaci.

Da yake magana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin ƙungiyar Hakeem Baba-Ahmed ya ce Buhari "ba zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabe mu ba".

"Da alama gwamnatin Buhari ba ta da abin cewa game da ƙalubalen tsaro da muke ciki. Ba zai yiwu mu ci gaba da zama ƙarƙashin ikon masu kisa ba, da masu garkuwa da mutane, da masu fyaɗe, da miyagun da suka hana mu 'yancinmu na zama lafiya," a cewar ƙungiyar.

"Kundin tsarin mulkinmu ya tanadi yadda shugabanninmu za su sauka daga mulki idan suka gaza ko kuma saboda wani dalili na ƙashin-kai," in ji NEF. "Loƙaci ya yi da ya kamata Buhari ya fara tunanin wannan zaɓin."

Sai dai gwamnatin ta mayar da martani ta bakin kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu cewa "saukar Buhari ba za ta magance matsalar tsaro ba", tana mai cewa an siyasantar da matsalar.



Read full article

Source: BBC
Related Articles: