BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Harin Yauri: 'Yan bindiga sun sace dalibai da dama a jihar Kebbi

Katsina Map Nigeria.jpeg Jihar Kebbi na arewa maso yammacin Najeriya

Fri, 18 Jun 2021 Source: BBC

Bayanai daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai da dama daga Kwalejin Tarayya da ke Yauri.

Ganau sun ce 'yan bindigar sun tafi da daliban da yawa sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin tarayya Muhammad Bello Ingaski ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun sace dalibai maza da mata da tsakar ranar Alhamis.

Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya gaya mana cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar sannan suka kwace motoci kirar Toyota Hilux wadanda suka zuba daliban sannan suka tafi da su.



Read full article

Source: BBC