BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Harin da aka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna ya fusata 'yan Najeriya

 123942527 B18dc0ec B9d0 4ad8 80e6 Eb531f37b0e7 Jirgin ƙasa na An=buja zuwa Kaduna

Tue, 29 Mar 2022 Source: BBC

Harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da daddare ya ɗaga hankulan ƴan Najeriya tare da sanya fargaba a zuƙatan mutane da dama.

Al'amarin ya jawo asarar rayuka da har yanzu hukumomi ba su fadi yawansu ba, sannan wasu sun jikkata sakamakon buɗe wuta da maharan suka yi bayan da jirgin ya taka bam din da suka dasa a kan hanyarsa.

Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a ƙasar da kuma ta ɗimauta mutane, musannan ganin akwai a ƙalla fasinjoji 970 a cikin jirgin.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ƙasar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.

Hakan ne ya sa mutane suka fi raja'a da bin jirgin ƙasan ganin yadda ya zama wata hanyar sufuri da mutane suke ganin ita ce mafi tsaro, fiye da bin hanyar mota, yayin da jirgi kuma ya yi tsadar da sai masu ido da kwalli ne za su iya biya.

A shafin tuwita an yi ta musayar ra'ayoyi inda aka yi amfani da maudu'an #Nigeria da #Kaduna sau kusan 100,000, a Facebook kuma a kalla sama da mutum 68,000 ne suka tattauna kan batun.

Tuni dai gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya kai ziyara asibiti don duba majinyatan, sannan kuma mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ma ya je jaje Kadunan.

Me mutane ke cewa?

Da dama ƴan Najeriyar da ke magana a kan batun sun fi nuna halin ruɗani da tashin hankalin da lamarin ya jefa su a cikin ne, musamman bayan yaɗuwar bidiyo daban-daban da ke nuna na cikin jirgin wasu jina-jina wasu kuma suna ta koke-koke.

Wasu kuma sun ta'allaƙa laifin harin ne a kan gwamnatin ƙasar, suna masu cewa ta daɗe da gazawa wajen shawo kan matsalar yaƙi da ƴan bindiga, musamman batun da ya shafi tare jirgin ƙasa wanda shi ne na biyu da maharan suka yi ƙoƙarin tare shi.

Duk da cewa dai na farkon ba su yi nasara ba kuma bai yi munin haka ba.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

Source: BBC
Related Articles: