BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Harin 'yan ta'adda a Mozambique: 'Ba zan iya komawa gida ba'

 124084760 Gettyimages 1235531467afp976 Soja a Mozambique | Hoton alama

Mon, 11 Apr 2022 Source: BBC

Garin Palma da ke arewacin Mozambique ya fuskanci wani mummunan harin masu ikirarin jihadi a bara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa, ya kuma tilasta wa dubbai barin muhallansu ya kuma tsayar da aikin samar da iskar gas da ake yi. Wakiliyar BBC a Afirka Catherine Byaruhanga ta tattauna da wasu da suka tsira daga harin domin jin mene ne ya sauya.

Har yanzu akwai tsoro da firgici a Palma.

Kafin a fara wannan tsararren harin, garin da ke gabar teku ya samu karbuwa daga mutanen da ke neman aiki a masana'antar gas.

Kuma akwai dubban mutane da suka tserewa rikicin wasu yankunan irinsu Carbo Delgado, shi ne babban garin Musulmai kuma daga nan ikirarin jihadi ya samo asali a 2017.

'Yan bindigar ana kiran su da suna al-Shabab. Amma ba su da wata alaka da waccan kungiyar ta Somaliya da ke da irin sunan, amma tun daga nan suke neman alaka da kungiyar IS.

A yau, kamfanin makamashi na Faransa Total da ke aikin miliyoyin daloli ya rufe.

Wadanda suka fara komawa gida yanzu a firgice suke, suna tsoron su yi magana da BBC ta waya ma, duk kuwa da cewa an kori 'yan bindigar daga yankin.

Antonio, daya daga cikin 'yan kwangila, ya je garin domin aiki da masana'anta gas, ba shi da wani kwarin gwiwar cewa rayuwa za ta yi kyau a nan gaba.

Duk da cewa an kai dakarun tsaro yankin domin su yaki al-Shabab, mutumin dan shekara 36 da muka sakaya sunansa saboda tsaro, ya ce ba zai iya komawa yankin ba.

"Ba na jin zan iya komawa can," kamar yadda ya shaida mani ta manhajar Zoom daga gidansa da ke kudancin Mozambique, inda a can ma yake ta faman neman aiki.

Ya fada cikin mummunar damuwa game da faruwar lamarin, na kwanaki hudu da aka kwashe daga ranar 24 ga watan Maris aka zagaye garin, ya ga 'yan bindigar sun karya kofar shiga inda yake aiki shi da kaninsa daga Zimbabwe zuwa Afrika Ta Kudu - inda suka boye kansu.

"Na ji harbin bindiga, da kabbara!' lokacin da na leko ta jikin labulena, na ga wani mutum guda da bindiga a kofar shiga gidan da nake, suna sanye da korayen tufafi da jan kyalle a kansu."

Dan bindigar ya kasa bude kofar da mutane 16 ke ciki, ciki har da kaninsa amma kuma an gano sun kulle kansu a dakin.

"Suka fara ihu: suna mun gano mutane, mun gano su, ku zo, ku zo!" cikin abubuwan da yake tunawa.

'Yan bindiga tara suka kama su suka kai su daji suka kashe su.

Antonio, wanda daga karshe aka ceto shi ta jirgin sama, ya ce har yanzu ba a ga gawar 'yan uwansa ba balle a mayar da su ga iyalansu.

"Al-Shabab hadari ne, babu abin da zai iya dakatar da su," in ji shi.

An ci gaba da tashin hankali

Hare-haren da ake kai wa Palma sun sanya Mozambique ta amince da taimakon kasashen waje. A watan Yuli, kimanin sojojin Rwanda 2000, da kuma na wasu kasashen Kudancin Afrika 1,000 sun isa Cabo Delgado.

Cikin makonnin, suka kakkabe mayakan al-Shabab daga wuraren da suke da karfi.

Amma wannan na nufin mayakan sun koma cikin dazuka da yankunan da ke da kusanci.

"Ta sauya yadda ake kai hare-hare - ta sauya tsarin yakin, amma an ci gaba da yakin," in ji Eric Morier-Genoud, wani mai sharhi a Mozambique masanin tarihi a Jami'ar Queen Belfast.

Wesley Nel, wanda dan Afrika Ta Kudu ne kuma yana cikin yan kasashen wajen da aka tsare a kawanyar da aka yi wa Palma, ya amince da hakan.

Cikin wani kokarin tserewa, shi da wasu mutum 100 sun yi kokarin ficewa daga otel din da suke kusa da teku. Amma a can ma 'yan bindigar na can suna jira, kuma sun kashe dan uwansa.

"Kullum ina tuna jerin gwanon motocin, a kokarin da suke yi na gudu abin da yakai ga harbin kanina... ina na tuna abin na tayar mani da hankali.

"A duk cikin kwanaki uku ko biyu, sai 'yan bindigar sun kai hari. Abin nan bai kare ba. Kamar dai ba a damu da lamarin ba. Idan kama Afrika babu wanda ya damu da kai."

Kwararren dan jaridar nan na Uganda Charles Onyango-Obbo, wanda ya ziyarci Palma a ya ce rayuwa na komawa kamar yadda take a baya a yankin sannu a hankali.

Wannan wata alama ce ke nan cewa Tolat zai dawo?

Ukraine ta saya tunanin

Manajan Total a Mozambique Maxime Rabilloud a kwanakin baya ya ziyarci kasar. Amma ya ce abin da ya faru a bara - da kuma sukar da Total ya sha na gaza kare mutanen da aka kai wa hari, ya sanya kamfanin yin kaffa-kaffa a yanzu.

Kullum ana cewa cewa gwamnati ce da hakkin samar da tsaro.

"Komai ya danganta ne a bisa daidaito da kuma ginin da aka yi wa tsaro," in ji Total.

Kimanin mutum 770,000 ne suka tsere daga yankin sakamakon rikicin, kuma har yanzu gwamnati na cewa kar su koma yankunan, a tunaninta har yanzu tsaro bai wadata ba.



Read full article

Source: BBC