BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Jacob Zuma: An tura sojoji don tarwatsa masu zanga-zanga a Afirka Ta Kudu

 119355673 Hi068497267 An yi ta fasa shaguna tare da ƙona gine-gine ranar Litinin

Tue, 13 Jul 2021 Source: BBC

Afirka Ta Kudu ta tura sojoji domin daƙile zanga-zangar da magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasar Jacob Zuma suka tayar game da ɗaurin da wata kotu ta yi masa.

An yi ta fasa shaguna tare da ƙona gine-gine ranar Litinin yayin da Mista Zuma ke ƙalubalantar ɗaurin a babbar kotun.

Mutum aƙalla shida aka kashe sannan aka kama 200 tun bayan ɓarkewar rikicin a makon da ya gabata.

An yanke wa Zuma hukuncin zaman gidan yari ne sakamakon kama shi da laifin raina kotu, inda ya ƙi halaratar wani zama game da zarge-zargen cin hanci da gwamnatinsa ta aikata a lokacin da yake kan mulki.

Ɗan shekara 79 wanda ya musanta zarge-zargen, ya miƙ kan sa ga 'yan sanda a makon da ya gabata domin fara aiwatar da ɗaurin na wata 15.

Yana fatan a janye ɗaurin ko kuma a rage yawansa a Kotun Tsarin Mulkin. Sai dai ƙwararru kan harkokin shari'a sun ce da wuya ya samu hakan.

Shari'ar ta janyo ce-ceku-cen da ba a taɓa gani ba a Afirka ta Kudu, wadda ba a taɓa ganin an ɗaure tsohon shugaban ƙasa ba.

Wani bidiyo ya nuna yadda aka cinna wa wani babban kantin sayar da kayayyaki a birnin Pietermaritzburg, inda nan ce nahaifar Mista Zuma da ke yankin KwaZulu-Natal, sannan mutane suka wawashe kayayyakin.

Wakiliyar BBC Nomsa Maseko lamarin ya ƙazanta a birnin. Masu zanga-zanga sun mayar da martani da harsashi mai kisa a lokacin da 'yan sanda suka harba musu na roba domin tarwatsa su a wani kantin wanda aka yashe da tsakar dare, a cewarta.

Rundunar soja ta ce dakarunta za su taimaka wa sauran jami'an tsaro "don daƙile tashin hankalin da ya addabi [dukkan] yankuna biyu a 'yan kwanakin da suka wuce".

Shugaabn Ƙasa Cyril Ramaphosa ya nemi a kwantar da hankali, yana mai cewa babu wani dalili na tayar da fitina.

Tun bayan gurfanar da shi a gaban kotun, sau ɗaya Zuma ya bayyana gabanta game da zargin karkatar da kuɗin ƙasa.

A wata shari'ar daban, ya musanta aikata laifi a watan da ya gabata, inda ake zargin sa da badaƙalar dala biliyan biyar na sayen makamai a shekarun 1990.

Magoya bayansa sun haƙiƙnce cewa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne ake yi masa, wanda suke zargin abokan Shugaba Ramaphosa da ƙulla masa.



Read full article

Source: BBC