BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Jadon Sancho: Man United ta gwada koshin lafiyar dan kwallon Ingila

 119389680 Gettyimages 1232871074 Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Manchester United

Tue, 13 Jul 2021 Source: BBC

Jadon Sancho na daf da kammala komawa Manchester United kan fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund, bayan da aka auna koshin lafiyarsa ranar Talata.

Ranar 1 ga watan Yuli, United ta amince da kudin da Dortmund ta gindaya kan dan wasan mai shekara 21, amma sai da aka kammala Euro 2020, sannan za a karkare cinikin.

Ranar Talata Sancho ya je filin atisayen United da ke Carrington da sanyi safiya, ana kuma sa ran kungiyar za ta sanar da karkare komai cikin makon nan.

Sancho tsohon dan kwallon Manchester City yana daga cikin wadanda suka kasa ci wa Ingila fenariti a Euro 2020 da ta kai Italiya ta lashe kofin.

Sauran da barar sun hada da Bukayo Saka da kuma Marcus Rashford, bayan da suka tashi 1-1 a Wembley ranar Lahadi.

Dan kwallon abokine ga Phil Foden a Manchester City tun kan ya koma Dortmund a 2017, sai dai Sancho bai buga wa babbar kungiyar City karawa ba.

Babban wasa da ya buga a Ingila a kungiya shine wanda Tottenham ta doke kungiyarsa Dortmund a Wembley a cikin watan Fabrairun 2019.

Sancho ya yi rauni a karawa biyu tsakanin Dortmund da Manchester City a quarter-final a Champions League a kakar da ta kare.



Read full article

Source: BBC