Karo na biyu kenan da Italiya ta zama zakara a gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai, bayan bajintar da ta yi a 1968.
Tun farko sun tashi 1-1 daga nan aka yi karin lokaci, nan ma ba samu gwani ba, dalilin da aka yi bugun fenariti, inda Italiya ta yi nasara da ci 3-2.
An fara gasar cin kofin nahiyar Turai a 1960, kuma Faransa ce ta fara karbar bakuncin karawar farko da Soviet Union ta lashe kofin, wadda yanzu ake kira Rasha, sai Yugoslavia ta karkare a mataki na biyu,
Tun cikin shekarar 2020 ya kamata a buga gasar Euro 2020, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasannin juwa cikin Yuli da aka kammala a Yulin 2021.
Ga jerin kasashen da suka lashe kofin nahiyar tun daga 1960:
Euro 1960
Mai masaukin baki: Faransa
Wadda ta lashe kofin: Soviet Union
Wadda ta yi ta biyu: Yugoslavia
Euro 1964
Mai masaukin baki: Sifaniya
Wadda ta lashe kofin: Sifaniya
Wadda ta yi ta biyu: Soviet Union
Euro 1968
Mai masaukin baki: Italia
Wadda ta lashe kofin: Italy
Wadda ta yi ta biyu: Yugoslavia
Euro 1972
Mai masaukin baki: Belgium
Wadda ta lashe kofin: Jamus
Wadda ta yi ta biyu: Soviet Union
Euro 1976
Mai masaukin baki: Yugoslavia
Wadda ta lashe kofin: Czechoslovakia
Wadda ta yi ta biyu: Jamus
Euro 1980
Mai masaukin baki: Italia
Wadda ta lashe kofin: Jamus
Wadda ta yi ta biyu: Belgium
Euro 1984
Mai masaukin baki: Faransa
Wadda ta lashe kofin: Faransa
Wadda ta yi ta biyu: Sifaniya
Euro 1988
Mai masaukin baki: Jamus
Wadda ta lashe kofin: Netherlands
Wadda ta yi ta biyu: Soviet Union
Euro 1992
Mai masaukin baki: Sweden
Wadda ta lashe kofin: Denmark
Wadda ta yi ta biyu: Jamus
Euro 1996
Mai masaukin baki: Ingila
Wadda ta lashe kofin: Jamus
Wadda ta yi ta biyu: Jamhuriyar Czech
Euro 2000
Mai masaukin baki: Belgium da kuma Netherlands
Wadda ta lashe kofin: Faransa
Wadda ta yi ta biyu: Italia
Euro 2004
Mai masaukin baki: Portugal
Wadda ta lashe kofin: Girka
Wadda ta yi ta biyu: Portugal
Euro 2008
Mai masaukin baki: Austria da kuma Switzerland
Wadda ta lashe kofin: Sifaniya
Wadda ta yi ta biyu: Jamus
Euro 2012
Mai masaukin baki: Poland da kuma Ukraine
Wadda ta lashe kofin: Sifaniya
Wadda ta yi ta biyu: Italia
Euro 2016
Mai masaukin baki: Faransa
Wadda ta lashe kofin: Portugal
Wadda ta yi ta biyu: Faransa
Euro 2020
An yi gasar a wasu daga kasashen Turai
Wadda ta lashe kofin: Italia
Wadda ta yi ta biyu: Ingila
Read full article