BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kardashians: Ƴan matan gidan masu arziki da suka sauya duniya

 118787745 Kardash2 Bayan shekaru 14, an nuna zangon ƙarshe na shirin Keeping Up With the Kardashians

Mon, 14 Jun 2021 Source: BBC

Bayan shekara 14 da kuma fitowa ta 20, an nuna zangon ƙarshe na shirin Keeping Up With the Kardashians a wannan makon.

Ana kallon shirin a ƙasashe da dama, shirin kuma ya sa masu shirin sun zama fitattu Kim Kardashian West, da mahafiyarta Kris Jenner, da ƙanwarta Kourtney da Khloe da Kendall da kuma Kylie.

Mujallar Forbes ta bayyana cewa arzikin Kim ya kai dala biliyan ɗaya, shirin ya ƙara azurta su.

Ko da ba ka ƙaunarsu, ba za ka iya musanta tasirin da suka yi ba a duniya.

Ga hanyoyi bakwai da ke tabbatar da tasirinsu.

1. Suna da gaskiya - da ban dariya

Ɗaya daga cikin nasarorinsu ya samo asali ne daga yadda suke bayyana kansu ba ɓoyo.

"Sun yi wasa da gara juna da gangan," in ji Dr Meredith Jones ta Jami'ar Brunel University a London, yayin da take bayyana yadda suka ja hankalin masu kallo.

Dr Jones da ke shirin gabatar da maƙala ta biyu kan Kardashinan tana ganin akwai dalilai da yawa da ya sa shirin ya yi nasara da samun karɓuwa.

"Mutane ba wai sun ɗauki ƴan Kardashians a matsayin masu ban dariya ba kawai, suna kallonsu a matsayin waɗanda suka ƙware wajen shirin ban dariya," in ji ta.

2. Sun sauya tunani kan 'kyakkyawar mace'

"Zan iya cewa Kim ya yi wani tasiri kan tunanin da duniya take da shi game da siffofin kyakkyawar mace," in ji Dr Jones.

"Daya daga cikinsu shi ne yadda ta gabatar da kanta a matsayin mai ci gaba."

Shirin ya fito da Kardashians a matsayin gamayyar waɗanda suka ƙware a fannoni da dama kamar kwalliya da ado da gyran gashi.

"Masu kallo za su tantance su da mutanen da suka yi kama da su idan har shirin ya kasance na nuna tsayi da siriran mata, ina ganin da ba zai samu nasara kamar haka ba," a cewar Dr Jones.

Amma ta nuna cewa, a shekarun baya musamman fitowar Kardashians bai nuna wata alama da alaƙa ba.

"Akwai iyaka kuma ina ganin masoyansu sun fahimci haka."

Amma wasu kan bi ta ko wace hanya domin neman kyau.

Likitocin tiyata a Birtaniya a baya sun ce suna da "damuwa" game da masu neman ƙarin girman duwawu.

Amma hanyoyin da ake bi kamar dashe da allura sun zama ruwan dare a yanzu, amma ba a nuna ko suna tattare da haɗari ba.

"A tsakanin shekaru 15 zuwa 20 za mu fara ganin abin da zai biyo baya musamman zamani da tsufa," in ji likitan tiyata Marc Pacifico.

Amma, ƴan Kardashians su da kansu suna cewa "ana yanke hukunci a kansu" kan yanayinsu.

A farkon wannan shekarar, Khloe ta yi ƙoƙarin cire hoto da ba a tace ba daga kafofin sada zumunta saboda tana ganin ba za ta iya "jure wa" matsin lambar daga mabiya.

"A gaskiya, matsin lamba da yanke hukunci kan rayuwata baki ɗaya don zama ta gari kuma bi tsarin wasu game da yadda ya dace na kasance wani abu ne da ba zan iya ɗauka ba," kamar yadda ta bayyana a shafukan sada zumunta.

Kardashians sun ja hankali a kafofin sada zumunta - shafukan Kylie da Kim suna cikin jerin shafuka 10 da aka fi bibiya a Instagram, yayin da Kendall da Khloe da Kourtney suke cikin manya 20 da aka fi bibiya.

Ga ra'ayin Dr Jones, sun yi "fice" ne, suna tsara yadda dukkaninmu ya kamata mu yi amfani da kafofin sada zumunta wajen gabatar da cikakkun bayanai game da mu da kuma hotunanmu.

"Ba yadda za a raba hotunansu da nasarar da suka samu da kuma nasarar Instagram," in ji ta.

3. Sun nuna wani yanayi na ƴan uwantaka

ɗaya daga cikin tasirin fallasa rayuwar gidanku ga ma'aikatan talabijin shi ne cewa za a iya jefa masu kallo cikin rikici na dangantaka.

Ga magoya baya da dama, wannan muhawarar ta fi ja hankali.

"A ko da yaushe suna burge ni kasancewar su dangi da za su iya faɗa kuma suna son juna," in ji Misis Jarreau.

"Duk da cewa mutane suna son yin magana game da su da ba su da tarbiya, a gaskiya ina ganinsu wasu mutanen kirki ne da za ka so ka kalla a talabijin."

Caitlyn, tsohuwar 'yar wasan Olympic, a baya ta ce "asalin yanayinta " ita ce babbar nasarar da ta samu.

"Na samu hoto na shekaru 12 don wasannin Olympic. Na samu hoto na shekaru 65 don sauyawa a 2015," kamar yadda ta shaida wa BBC.

"Kowa na son wasannin. Mutane da dama a lokacin da suka ga ka sauya lokacin ne suke jin ƙyashinka. Dubi maganganun da ake shafin Instagram. A yanzu ya fi ƙalubale.

Caitlyn ta kuma sami kyaututtuka da dama saboda da'awarta.

Amma kuma ta fuskanci suka daga wasu ƴan fafutika saboda siyasarta da kuma goyon bayanta ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

4. 'Wariya da dacewar al'adu

Idan Kardashians sun nuna bambancin rayuwa a Amurka, to da sun bayar da wata da dama da nuna wani abin da bai dace ba na al'umma.

An zarge su da lalata al'adu da kuma abin da ake kira "sauya kamanni zuwa baƙar fata". Wato lokacin da wani yake fake wa shi baƙar fata ne ko ruwa biyu, musamman a kafofin sada sadarwa na intanet.

"Daga jikinsu, zuwa sutura, har zuwa yadda suke gyara gashinsu, sun bayar da dama ga wasu al'adu, musamman al'adun baƙar fata," in ji Ms Jarreau.

"Ana kallon Kardashians a matsayin farare kuma baƙar fata," in ji Adria Y Goldman, farfesar sadarwa a Jami'ar Mary Washington.

5. An tabka soyayya - da rabuwa

An nuna soyayya sosai a shirin tsakanin Kim da Kanye West, Khloe da Tristan Thompson da Kylie da Travis Scott, kuma dukkansu suna da ƴaya tare.

Dr Jones ya ce, ƴa Kardashians suna " sun nuna wannan yanayin dangantakar mai gamin gambiza".

"Duk matsalolin da suka samu, da wahala mu iya alaƙanta nasabar wata al'umma ko kabila."

Amma yayin da ake gabatar da wannan dangantakar a shirin mai cike da ce-ce-ku-ce.

Kamar yadda Farfesa Goldman ya nuna, soyayyar da ke tsakanin Kim da Kanye ta janyo muhawara al'adun baƙar fata.

"Alaƙarta a Kanye da ƴaƴansu ya nuna matsayinta nuna kamannin farar fata da baƙar fata," in ji ta.

"Wasu na ganin da ƴaƴan Kim da Kanye su ba ta damar yin amfani da al'adun baƙar fata."

6. Zargin yin facaka da dukiyoyinsu

Kim a baya ta yi magana game da tasirin Kanye a kan kasuwancinta kuma ta yaba masa kan yadda ya sauya halinta.

"Kawai ya koya min a matsayina na mutum kada na taba yin sassauci ba kuma ƙoƙarin mallakar dukiya," kamar yadda ta shaida Forbes

"A baya, na kasance akasin haka. Zan iya sa sunana a kan komai."

Wani ɓangare na ƙarshe a shirin an yi shi ne lokacin annobar cutar korona kuma nuna dukiya ya kasance wani mafi ƙalubale ga masu kallo.

"Tafiye-tafiye na tsibirai masu zaman kansu, da kashe yin facaka, kuma tare da dukkanin ma'aikatansu da yin kwalliya yadda suka saba yayin da ake cikin wahala a lokacin korona."

7. Sun shirya yin rayuwa ta gaskiya bayan shirin na talabijin

Duk da Keeping Up With the Kardashians zai ƙare, amma sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da wani kamfanin Amurka na Hulu kuma za ƙaddamar da shirinsu a wannan shekarar.

Ba a yi cikakken bayani ba game da shirin, amma da alama za mu ji karin bayani game da makmar Kim da Kanye.

Yanzu za su ci gaba da nemam dammakinsu bayan shirin na talabijin.

"Kim ta fi dacewa da samun nasarori fiye da saura," in ji Dr Jones.

"Ta ce da zarar ta kammala karatunta na lauya, za ta bude kamfaninta da zai mai da hankali kan yanke hukunci da sake fasalin gidan yari."



Read full article

Source: BBC