BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Karim Benzema ya zama na hudu a cin kwallaye a Champions League

 120737529 Mediaitem120737525 Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid

Thu, 30 Sep 2021 Source: BBC

Karim Benzema ya zama na hudu a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Champions League.

Dan wasan tawagar Faransa shine ya ci wa Real Madrid kwallo a wasan Champions League da Sheriff ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Hakan ya zama na hudu a yawan cin kwallaye da 72 a raga, ya kuma hau kan Raul mai 71 a tarihin zazzaga kwallaye a Champions Leguea.

Cristiano Ronaldo ne kan gaba a cin kwallaye a gasar mai 135, sai Lionel Messi na biyu mai 121, wanda ya ci Manchester City a karawar da Paris St Germain ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata.

Dan wasan Bayern Munich,, Robert Lewandowski shine na uku a yawan cin kwallaye a Champions League mai 75 a raga.

Benzema ya fara kakar bana da kafar dama, wanda kawo yanzu ya ci kwallo takwas a gasar La Liga ya kuma bayar da bakwai aka zura a raga.

Ba wani dan kwallon Faransa da ya ci kwallo da yawa a Champions League, Thierry Henry ya zura 50 a raga a gasar ta Zakarun Turai.

Mai shekara 33, shine na biyar a jerin wadanda ke kan gaba a ci wa Real Madrid kwallaye mai 288, kuma daf yake ya hau kan Carlo Santillana mai 290.

Haka kuma Cristiano Ronaldo shine kan gaba a yawan cin kwallaye a Real Madrid mai 451, sai Raul na biyu mai 323 da kuma Alfredo Di Stefano na uku mai 308 a raga.

Kawo yanzu Benzema ya zura kwallo 200 a La Liga, hakan na nufin saura 16 ya kamo Di Stefano da kuma tara tsakani ya yi kan-kan-kan da Raul.

Kawo yanzu Cristiano Ronaldo shine na daya dai a Real Madrid a zura kwallaye a gasar La Liga mai guda 312.



Read full article

Source: BBC