BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Gabriel Jesus, Pogba, Dest, Godfrey, Osimhen da Carrick

 124700627 Mediaitem124700626 Gabriel Jesus

Thu, 12 May 2022 Source: BBC

Juventus a shirye take ta ba dan wasan tsakiya na Manchester United da Faransa Paul Pogba fan miliyan takwas a shekara wanda ya kai kusan fan 160,000 a mako da karin wani babban kunshin kudi don sa hannu.

Kwantiragin Pogba da United zai kare a bazara kuma Manchester City na son dauko dan wasan mai shekara 29. (Mirror)

Chelsea na zawarcin dan wasan bayan Barcelona da Amurka Sergino Dest, mai shekara 21. (Sport Spanish)

Wakilin dan wasan gaban Brazil da Manchester City Gabriel Jesus ya tabbatar da cewa dan wasan mai shekara 25 ya tattauna da Arsenal kan yiwuwar komawa kungiyar. (Guardian)

Shirye-shiryen sayen 'yan wasa na Manchester United na cikin rudani bayan da 'yan wasan tsakiya uku da suke son siya a bazara suka ki amincewa da komawa Old Trafford. (Star)

Tottenham na zawarcin 'yan wasan Everton uku da suka hada da dan wasan gaban Brazil Richarlison, mai shekara 25, da dan wasan gefe na Ingila Anthony Gordon, mai shekara 21, da kuma dan bayan Ingila Ben Godfrey mai shekara 24. (Telegraph)

Spurs din na kuma zawarcin dan wasan tsakiya na Leicester da Belgium Youri Tielemans, mai shekara 25. (GiveMeSport)

Dimitar Berbatov ya shaida wa tsohon kulob dinsa na Tottenham cewa kada su mayar da hankali wajen ganin sun ci gaba da rike kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 28, a bazara shi kadai, saboda manyan kungiyoyi za su sa ido kan dan wasan Koriya ta Kudu Son Heung-min Heung, mai shekara 29, shi ma. (London Evening Standard)

An shaida wa Manchester United cewa dole ne ta biya sama da Yuro miliyan 85 idan tana son sayen dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 23, daga Napoli a bazara. (Calciomercato)

Aston Villa na dab da sanar da sayen dan wasan Brazil da Barcelona Philippe Coutinho a matsayin dindindin. (Fabrizio Romano)

Leicester tana son dauko dan wasan Club Bruges da Belgium Charles de Ketelaere, mai shekara 21. (Corriere dello Sport)

Southampton na tunanin zawarcin golan Fiorentina da Poland Bartlomiej Dragowski, mai shekara 24. (Telegraph)

Crystal Palace na son sayen dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher, mai shekara 22, a matsayin dindindin bayan ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kulob din a kakar wasa ta bana a matsayin aro a kulob din.(Talksport)

Tsohon dan wasan Manchester United da Ingila Michael Carrick, mai shekara 40, ya fi so ya zama kocin Lincoln City na gaba. (Football Insider)



Read full article

Source: BBC