BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Pochettino, Osimhen, Jesus, Dybala da Elneny

 124277075 Mediaitem124277074 Victor Osimhen

Mon, 25 Apr 2022 Source: BBC

Paris St-Germain na shirin korar kocinta Mauricio Pochettino, yayin da ake sa ran kocin Tottenham Antonio Conte zai maye gurbinsa (Le Parisien)

Chelsea na iya sake duba yiwuwar zawarcin dan wasan bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 23, a bazara bayan da aka tabbatar Antonio Rudiger zai bar kungiyar. (Football London)

Arsenal ta dauki matakin sayen dan wasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 23. (Gazzetta dello Sport)

Dan wasan gaban Manchester City Gabriel Jesus, mai shekara 25, ya ki amincewa da tsawaita zamansa har zuwa bayan karshen kakar wasa ta bana. (Guardian)

Arsenal ta yi imanin za ta iya kammala cinikin dan wasan na Brazil a bazara. (Mail)

Chelsea da Tottenham na zawarcin dan wasan gaban Inter Milan Martin Satriano, mai shekara 21. Dan kasar Uruguay din yana zaman aro a kulob din Brest na Faransa. (Mirror).

Dan wasan tsakiya na Brazil da ke da alaka da Newcastle Lucas Paqueta, mai shekara 24, ya shaida wa kulob dinsa na Lyon cewa zai yanke shawara kan makomarsa a karshen kakar wasa ta bana. (Evening Chronicle)

Leeds ta aike da 'yan kallo don kallon dan wasan baya na Cologne na Jamus Timo Hubers, mai shekara 25. (Insider Football)

Roma ta shiga zawarcin dan wasan Juventus da Argentina Paolo Dybala, mai shekara 28. (Fichajes Spanish)

Real Betis na kokarin dauko dan wasan Real Madrid da Spain Isco, mai shekara 30. (Marca)

Dan wasan tsakiya na Masar Mohamed Elneny, mai shekara 29, ya ce zai rattaba hannu kan sabon kwantiragi a Arsenal ko da ba a ba shi tabbacin lokacin taka leda ba. (Irish Examiner)



Read full article

Source: BBC