BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos, Otavio, Bale, Camavinga, Patricio, Belotti

 119128485 Ramos Getty Index Sergio Ramos

Tue, 29 Jun 2021 Source: BBC

Mai tsaron bayan tawagar Sifaniya, Sergio Ramos, mai shekara 35, na duba kungiyar da ya kamata ya koma kafin ya yanke hukunci, bayan da Manchester City da Paris St-Germain da kuma Bayern Munich ke zawarcinsa. (ESPN).

Tottenham Hotspur ba ta da damar tsawaita yarjejeniyar dan wasan tawagar Wales Gareth Bale wanda ya buga ma ta wasannin aro a kakar da ta kare, inda dan wasan mai shekara 31 zai koma Real Madrid, wadda saura kaka daya kwantiraginsa ya kare a kungiyar. (Evening Standard)

Rennes ta ce ba wata kungiya da ta taya dan kwallon tawagar Faransa, Eduardo Camavinga a wajenta, duk da ana alakanta dan wasan mai shekara 18 da cewar zai koma taka leda Manchester United ko kuma a Paris St-Germain. (Metro)

Roma ta kusan kulla yarjejeniyar daukar mai tsaron ragar Portugal, Rui Patricio, mai shekara 33, daga Wolves. (Sky Sports)

Arsenal na son daukar dan kwallon Torino da tawagar Italiya, Andrea Belotti, sai dai AC Milan da Fiorentina da Napoli da kuma Roma na son mallakar dan wasan mai shekara 27. (Tuttosport, via 90Min)

Kungiyar Arsenal da Everton da kuma Tottenham na rige-rigen daukar dan kwallon Inter Milan dan kasar Uruguay Martin Satriano, mai shekara 20. (Mail)

Leicester City na daga cikin kungiyoyin da ke son sayen matashin dan wasa mai shekara 26 dan wasan Italia Domenico Berardi, wanda ke taka leda a Sassuolo. (Gazzetta Dello Sport, via Leicester Mercury)

Norwich City ta kusan daukar aron dan wasan tawagar Scotland, Billy Gilmour, mai shekara 20 daga Chelsea. (Sky Sports)

Watakila Liverpool ta dauki dan wasan Porto dan kasar Brazilian, Otavio, mai shekara 26, kafin ranar Laraba kan fam miliyan 34 kudin kunshin yarjejeniyarsa ke nan. (Star)

Barcelona na duba yiwuwar bai wa dan kwallon Sifaniya, mai shekara 29 Sergi Roberto yarjejeniyar kaka biyu, wanda kwantiraginsa za ta kare a Camp Nou a karshen kakar 2022. (Marca)



Read full article

Source: BBC