BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Mbappe, Pogba, Varane, Kessie, Hazard, Xhaka

 119543693 714e5d43 B541 4791 8858 6b4d4a0ba831 Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila

Fri, 23 Jul 2021 Source: BBC

Manchester City a shirye take ta bayar da daya daga cikin zaratan 'yan wasanta na gaba bayan kudi domin Tottenham ta sayar mata kyaftin din Ingila Harry Kane.

Daya daga cikin 'yan wasan da Manchester Cityn za ta bayar su ne dan Brazil, Gabriel Jesus, mai shekara 24 ko kyaftin din Aljeriya Riyad Mahrez, mai shekara 30 ko dan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva, mai shekara 26 ko kuma Raheem Sterling, na Ingila mai shekara 26. (FourFourTwo)

Ana ganin Kane zai rika karbar albashin fam dubu 400 a duk sati a yarjejeniyar da Manchester City take son ta kulla da shi idan Tottenham, ta sayar mata da shi. (Jaridar Sun)

Dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, zai yi watsi da tayin kwantiragin da Paris St-Germain za ta sake yi masa saboda hankalinsa ya riga ya tafi Real Madrid, duk da kokarin kungiyar ta Faransa na dauko abokin wasansa na tawagar Faransa, dan Manchester United Paul Pogba mai shekara 28. (Marca - in Spanish)

Ana sa ran Pogba ya bar Manchester United a bazaran nan bayan da ya yi watsi da tayin ba shi albashin fam dubu 350, a duk mako, inda kungiyar ta Premier ba ta son ya kari wa'adin yarjejeniyar zamansa, ya tafi kyauta a shekara mai zuwa, 2022. (Jaridar Mirror)

Haka kuma Manchester United din na kokarin cimma yarjejeniya da Real madrid kan sayen dan bayan Faransa Raphael Varane, mai shekara 28. Kungiyar ta La Liga na bukatar fam miliyan 50 a kansa yayin da United ta ce fam miliyan 40 za ta bayar. (Mirror)

Liverpool na daya daga cikin kungiyoyin Turai da suke duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na AC Milan, dan Ivory Coast, Franck Kessie, mai shekara 24. (Gazzetta dello Sport)

Newcastle na da kwarin guiwar cewa za ta samu dan wasan tsakiya na Southampton kuma dan Gabon Mario Lemina, mai shekara 27, bayan tattaunawa da wasu 'yan wasan na tsakiya da dama wadanda sun yi wa kungiyar tsada. (Northern Echo)

Eden Hazard, mai shekara 30, ya riga ya nuna cewa babu maganar komawarsa Chelsea, bayan da kafafaen yada labaran Sifaniya suka bayar da rahoton Real Madrid ta yi wa Chelsea tayin mayar mata da shi. (Mirror)

Sheffield United ta gaya wa Arsenal ta kara tayin da ta yi wa Aaron Ramsdale mai shekara 32, zuwa sama da fam miliyan 32 , bayan da kungiyar ta ki tayi biyu da Arsenal din ta yi wa mai tsaron ragar. (Times)

Atalanta na sha'awar sayen dan bayan Colombia Davinson Sanchez, mai shekara 25, a cinikin da zai iya kai wa ga dan bayan Argentina Cristian Romero, mai shekara 23,tafiya Tottenham a bazaran nan. (Gianluigi Longari)

Chelsea ta fara tattaunawa da dan bayan Ingila Dujon Sterling mai shekara 21 a kan sabuwar yarjejeniyar zamansa a kungiyar.

Hakan ya biyo bayan yabawar da jami'an Chelsea suka yi ne a kan farfadowar da dan wasan ya yi ne ya dawo wasa garau, bayan raunin da ya ji da zai iya kawo karshen wasansa. (football.london)

Haka kuma Chelsean na son daukar golan Argentine Sergio Romero, mai shekara 34,wand aba shi da kungiya bayan da kwantiraginsa da Manchester United yak are, a kokarin da Blues din suke yin a neman mai tsaron raga na uku da zai rika zaman ko-ta-kwana ga Edouard Mendy da Kepa Arrizabalaga. (Telegraph)

Dan wasan tsakiya na Arsenal Granit Xhaka na dab da kamala komawa Roma, inda kungiyar ta Serie A ta zaku kyaftin din na Switzerland mai shekara, 28, ya koma a kan lokaci su tafi da shi wasannin gwaji na tunkarar sabuwar kaka da za su yi a Portugal mako mai zuwa. (Daily Mail)

Watakila Aston Villa ta taya dan wasan gaba na kungiyar River Plate kuma dan Argentina Julian Alvarez mai shekara 21, a mako mai kamawa. (TNT Sports )

Newcastle da ke fafutukar sayen dan baya na na sha'awar dan bayan Tottenham da Amurka Cameron Carter-Vickers, mai shekara 23, bayan da Brentford ta yi nasarar saye dan wasan baya na Celtic da Norway Kristoffer Ajer, mai shekara 23. (90Min)



Read full article

Source: BBC