BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Salah, Kante, Christensen, Lewandowski, Origi, Antony, Timber

 123990871 300acf79 4ea1 45fc 8bcb B22bc218b330 Mohamed Salah

Mon, 4 Apr 2022 Source: BBC

Mohamed Salah, na dab da sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar zamansa a Liverpool har zuwa karshen sana'arsa ta kwalllon kafa. (Sunday Mirror)

Real Madrid na daga kungiyoyin da ke da sha'awar tattauna batun sayen N'Golo Kante na Chelsea, idan har za a sayar da dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 31, a bazarar da ke tafe. (AS - in Spanish)

Dan bayan Chelsea dan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, ya cimma yarjejeniya ta baka kan cewa zai koma Barcelona. (Football Insider)

Dan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya gaya wa Barcelona cewa yana son zuwa kungiyar a bazaran nan, idan har za ta ba dan wasan na Poland mai shekara 33 kwantiragin da ya wuce shekara biyu. (Sport - in Spanish)

Dan gaban Liverpool na Belgium Divock Origi, mai shekara 26, na dab da cimma yarjejeniyar shekara hudu da AC Milan. (Calciomercato - in Italian)

Erik ten Hag ya ware 'yan wasa biyu da yake son saye idan har ya zama kociyan Manchester United, kuma dukkaninsu daga kungiyarsa ta yanzu Ajax suke - dan Brazil Antony, mai shekara 22, da kuma dan Netherlands Jurrien Timber, mai shekara 20. (Sunday Mirror)

An gaya wa Manchester City da Liverpool cewa su bar maganar matashin dan wasan tsakiya dan Sifaniya Gavi, mai shekara 17, saboda yana shirin kulla sabuwar doguwar yarjejeniyar zamansa a Barcelona. (90min)

Haka kuma Barcan na fatan cimma yarjejeniyar tsawaita zaman Ronald Araujo a mako mai zuwa, saboda suna sane da yadda kungiyoyin Premier ke son dan wasan na Uruguay mai shekara 23. (Sport - in Spanish)

Liverpool na son sayen wani fitaccen dan wasan tsakiya a bazaran nan, kuma wanda kungiyar ke hari shi ne Declan Rice mai shekara 23,dan tawagar Ingila na West Ham. (Football Insider)

Leicester na tunanin sayar da dan wasanta na tsakiya dan Ingila wanda aka yi wa kudi fam miliyan 50, James Maddison, mai shekara 25, saboda sake fasalin kungiyar a bazaran nan. (Mail on Sunday)

Burin Manchester City na sayen dan wasan Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland, zai sa dan wasan tsakiya na Ingila Phil Foden shi ma mai shekara 21, ya samu Karin albashi a City din. (Daily Star Sunday)

Newcastle da West Ham da kuma Southampton dukkanninsu sun tattauna kan neman sayen dan West Brom, Sam Johnstone kuma yanzu Tottenham ta dawo kan neman mai tsaron ragar na Ingila, mai shekara 29. (Mail on Sunday)

Golan Arsenal dan Jamus Bernd Leno, mai shekara 30, zai yi watsi da bukatarsa da Newcastle ke yi maimakon haka zai koma gasar Bundesliga a bazaran nan. (Daily Star Sunday)

Kociyan Chelsea Thomas Tuchel na son sayar da Romelu Lukaku, da Timo Werner, na Jamus a bazaran nan. (Football Insider)

Napoli ta kara wa dan bayanta na Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 30, wa'adin zama har shekara ta 2025. (Nicolo Schira, Twitter)



Read full article

Source: BBC