BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Eriksen, Bale, Silva, Salah, Fernandez, Paqueta, Ocampos

Christian Eriksen   New Christian Eriksen

Sat, 16 Apr 2022 Source: BBC

Newcastle na son kafa tarihi wajen saye ɗan wasan BrentfordChristian Eriksen, don haka a yanzu ta shiga fafatawa da Tottenham, Everton da West Ham kan ɗan wasan tsakiyar mai shekara 30, yayinda ƙungiyar da ya ke takawa leda yanzu ke son tsawaita zamanta a yammacin Landan. (Northern Echo)

Corinthians, Botafogo da Flamengo sun tuntubi kyaftin ɗin Manchester City Fernandinho ko za su daidaita, bayan dan wasan mai shekara 36 ya sanar da anniyarsa ta bakwana da Etihad. Sai dai ɗan wasan asalin Brazil ya fi son ya koma tsohuwar kungiyarsa Athletico Paranaense. (Globo Esporte)

Liverpool ta amince ta biya ɗan wasanta Mohamed Salah £400,000 a kowanne mako a kokarin ganin ta ci gaba da tsugunar da ɗan wasan mai shekara 29 kyaftin ɗin Masar a Anfield.(Metro, via Football Insider)

West Ham ta shiga sahun masu farautar ɗan wasan Bayern Leverkusen Moussa Diaby. Ɗan wasan mai shekara 22 ya kasance wanda Liverpool ke sa wa ido idan aka samu akasi Salah yaƙi amincewa da tsawaita zamansa. (Liverpool Echo via Calciomercato - in Italian)

Tottenham da Cardiff na son saye ɗan wasan Wales Gareth Bale, idan kwantiraginsa ya kare a Real Madrid cikin watan Yuni. (Wales Online)

Tsohon ɗan wasan -Manchester City da ke bugawa Sifaniya tsakiya David Silva ana sa ran ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa da shekara guda a Real Sociedad, amma kungiyar na son zabtare masa albashi. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Edinson Cavani na iya kasance sirrin Manchester United na sayo ɗan wasan Uruguay Darwin Nunez daga Benfica a wannan kakar. (90 Min)

Ana alakantaArsenal da Newcastle da cinikin ɗan wasa daga Lyon Lucas Paqueta. A baya ɗan wasan na Brazil mai shekara 24 anyi ta cewa Paris St-Germain na zawarcinsa kan £58m. (Chronicle)

Manchester City na fuskantar gasa yayinda take sanya ido kan dan wasan River Plate Enzo Fernandez, mai shekara 21. (Ole - in Spanish)

Fernandez tuni ya tattauna da Manchester United da Real Madrid kuma yanzu yana da damar tafiya wata kungiyar kan euro miliyan 20 (£16.6m). (Express via Cesar Luis Merlo - in Spanish)

Aberdeen na kokarin daukan ɗan wasan Ipswich Town mai shekara 31 Vaclav Hladky, wanda a baya aka rinka alakanta shi da St Mirren. (Record)

Newcastle na gab da cimma yarjejeniya da matashin ɗan wasan nan mai shekara 17 da ke taka leda a Galway UnitedAlex Murphy. (RTE)

KocinRangers Giovanni van Bronckhorst na son dauko ɗan wasan Sunderland asalin Scotland Ross Stewart. (Daily Record)

West Ham da Wolves dole su biya Sevilla euro miliyan 70 (£58.1m) idan suna so a sakar musu ɗan wasan nan na Argentina Lucas Ocampos. (Super Deporte)

Arsenal na shirin mika tayin euro miliyan 20 kan dan wasan Galatasaray Kerem Aktürkoğlu. (Star Gazetesi - in Turkish)



Read full article

Source: BBC