BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ku San Malamanku tare da Malam Abubakar Lamido

 124175595 C0063t01 Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Abubakar Lamido

Sat, 16 Apr 2022 Source: BBC

Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

An haifi Malam Abubakar Lamido Abdullahi a shekarar 1955 a cikin Jihar Gombe.

Malam Abubakar wanda shi ne shugaban majalisar malaman Jihar Gombe na ƙungiyar Izala mai hedikwata a Abuja, an haife shi a fadar Sarkin Gombe Marigayi Abukatar - kakan sarkin Gombe na yanzu.

Mahaifinsa ma'aikaci ne a fadar sarki, inda ake kiran sa da Mabudin Gombe, wato wanda ke kula da dukiyar sarki.

Mahaifin malam ya sanya shi a firamare ta Tudun Wada a shekarar 1963. Ya kammala aji bakwai a shekarar 1969.

Daga nan ya tafi Goverment Arabic Teachers Collage a Gombe, inda ya fara a shekarar 1970, ya kuma kammala a 1974.

Daga nan aka dauke su aikin koyarwa a firamare. An mayar da shi ainahin makarantar Tudun Wada da ya yi, inda a nan aka ba shi aikin koyarwa.

''Akwai wani malaminmu da ke koya mana harshen Larabci, kuma dan uwa ne a gare ni, lokacin da aka bude gidan Rediyon Bauchi, sai suka bukaci wanda zai dinga gabatar da labarai da Filllanci, aka yi min gwaji daga nan kuma suka dauke ni aiki," in ji malamin.

"Ina cikin aikin nan, sai mai matarba Sarkin Gombe Marigayi Abubakar, ya shaida wa mahaifi na ba ya son aikin gidan Rediyo da nake yi. Don haka ya matsa sai da na koma gida. Sai na ci gaba da aikin koyarwar da na bari a dai makarantar Tudun Wada. Tafi-tafi har sai da na kai mukamin hedimasta a makarantar firamare mai suna Danlami."

Bayan shafe shekara 12 yana koyarwa, sai ya ji ya gaji da aikin don haka sai ya yi ritaya daga koyarwa a shekarar 1983.

Amma a shekarar 1986, an dauke shi aiki a Bauchi State Afgricultural Development Project a matsayin mai kula da rumbun adana kayayyaki.

''Sai aka tura ni kwalejin Bauchi na yi kwas na wata uku kan fannin akawu. Bayan nan na nemi Difloma a Jami'ar Bayero da ke Kano, na karancin Hausa Arabic da Islamic Studies, na kammala a shekarar 1995.

"Na so ci gaba da karatu, kuma Allah cikin ikonsa, sai na samu yin babbar difloma a ATBU. Daga baya na sake komawa ATBU din na yi HND a fannin Akawu. Na ci gaba da aiki amma ina nan a matsayin limamin masallacin Juma'a, ina karantarwa a gidana kuma na bude makarantar islamiyya na ci gaba da karatu na zaure."

Manyan malaman zaure da ya yi karatu a hannusu akwai Malam Usman Dan Gungu.



Read full article

Source: BBC