BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ku san Malamanku tare da Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe

 119317316 P09nql0j Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe

Sat, 10 Jul 2021 Source: BBC

Malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe, ya ce babban abin da yake sanya shi farin ciki shi ne idan ya je yin da'awa.

Malamin ya shaida wa BBC cewa a ko da yaushe yana taka tsan-tsan wajen fadin abin da zai taɓa mutuncin wani.

"Wajen ida sako, ina da dabarun da nake amfani da su cikin raha da annashuwa sai na yi sako-sako, mutane ba sa gane ya musu nauyi har sai na tafi," in ji shi.

Malamin ya bayyana cewa ya fuskanci kalubale da dama a tsawon lokacin da ya dauka yana yada addinin Musulunci.

"Babban kalubalen shi ne na je da'awa a gabana aka kashe mutume 11, jini ne kadai ya shafi jikina amma babu abin da ya same ni.

Sannan 'yan fashi da makami sun taɓa tare mu zan je wa'azi, da guntun wando na isa ofishin 'yan sanda. Na dade ina mafarkin wannan cikin iyalina, ina fadin ga su nan amma sai su ce Malam babu komai."

Malam Muhammad Tukur ya ce dalilin da ya sa da'awarsa ta fita daban shi ne "zamowa fitaccen malamin makaranta, to da'awarsa ta fita daban.

"Da yake ana fuskantar matsanancin talauci, to talakawa na jin dadi idan suka kewaye ni ina fadin a saki kalmomin a taimaka wa bayin Allah, a saki kayayyaki da sauransu, wannan ya sa mutane ke ƙaunar zama wajen wa'azina."

Tarihin Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe

An haifi Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe a garin Jangebe a ranar 26 ga watan Oktoba 1959, a masarautar Talatar Mafara da ke jihar Zamfara.

Ya fara karatun Alkur'ani a wajen kanin mahaifinsa Malam Muhammadu Ana Ruwa, daga nan zuwa ga kakansa Malam Alhassan a garin Gusau.

Amma inda ya yi karatu mai zurfi, shi ne a wajen Malam Abdurrahman Malam Ango Kalgawa a garin Gulma, inda ya shekara bakwai a hannunsa.

A nan ya koyi daukacin karatun Alkur'ani da rubuta shi da sauke shi, daga baya ya ci gaba da karatun littafan musulunci daga garin Gulma zuwa Sakkwato, da Zaria ya kuma dangana ga marigayi Sheikh Abubakar Gumi a jihar Kaduna.

Cikin ikon Allah ya samu gurbin karatu makarantar nazarin harshen Larabci da addinin Musulunci ta Sultan Abubakar da ke jihar Sakkwato.

Daga nan ya ci gaba da karatu a makarantar nazarin addinin Musulunci a harshen Hausa da Larabci CICAS duk dai a Sakkwato, bayan nan ya ci gaba da karatu a Jami'ar Usman Danfodiyo.

Farin jinin mata

Malamin ya kuma yi fice wajen mata a jihar Sakkwato saboda yadda yake da'awar a ba su hakkinsu da sauransu.

Malamin dan ƙwallo ne a zamanin kuruciyarsa, "Da kyar da sidin goshi kakana ya raba ni da ƙwallo, domin sai an tara yara za a yi karatu ni kuma ina can ina buga ƙwallo.

Shi ya sa a duk lokacin da na ji ana yi wa yara fada kan kwallon kafa sai dai na yi wa'azi ba na tsaurarawa domin ni ma ta dan debe ni."

Wani abu da ya tsaya masa a zuciya da ransa ke ɓaci duk lokacin da ya tuna, shi ne yi wa 'yan fashi addu'a.

"Lokacin ina unguwar Zabarmawa, 'yan fashi sun taba zuwa gidana lokacin ina cikin wahala ba na aikin komai, ina azumi sai na aika aka sayo min kunu na naira 100.

Sai suka zo suka ce suna son gani na har da tambayar yaya aka yi nake shan kunu, na ce ba ni da hali.

"Ashe ɓarayi ne ɓoye da bindiga, suka ce za a kawo min sadakar kudi da abinci na ba su tukwuici, na ce ba ni da komai, ba su cuce ni ba ko iyalina.

Sai gudan ya ce na raka shi, mu na fita sai ya yi shewa sai wani ya fito da babur ƙato sai ya hau, sai wani ya sake fitowa su uku.

"Suka ce malam a yi mana addu'a, na ce Ubangiji Allah ya tsare ku Allah ya kare ku, kawai sai ganin bakin bidiga na yi ta wajen danjar babur."

Iyali

Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe yana da mata da ƴaƴa 49. Amma a yanzu 28 ne a raye, yayin da 11 suka rasu.

Babban burin shi shi ne, "Allah ya sanya al'ummar Hausawa su hada kai, mu yi maganin rarrabuwar kawuna, mu kawo karshen barace-barace, rubuce-rubucen batanci na al'ummar Bahaushe, burina karshe na mutu na shiga aljanna."




Read full article
Source: BBC