BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ku san Malamanku tare da Ustaz Adam Muhammad Murtadha

 123632582 P0btpx9y Ustaz Adam Muhammad Murtadha

Sat, 12 Mar 2022 Source: BBC

Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daUstaz Adam Muhammad Murtadha:

An haifi Ustaz Adam Muhammad Murtadha a karamar hukumar Ajingi da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya a shekarar 1978.

Malamin ya soma karatunsa na allo a wurin mahaifinsa, Malama Murtala, wanda shi ma malamin addinin Musulunci ne. Daga bisani ya koma Unguwar Bachirawa da ke cikin birnin Kano, inda ya yi karatu a wurin wani fitaccen Malami mai suna Malam Garba.

Ustaz Adam ya kara da cewa bayan rasuwar mahaifinsa ya tafi Gombe wurin kakansa mai suna Malam Abdulhamid wanda aka fi sani da Malam Karami inda ya ci gaba da karatun Alkur'ani.

"Baya da Allah ya ba ni ikon samun karatun Alkur'ani, sai kuma na shiga makarantar gaba da firamare mai suna Government Arabic College, Gombe, inda na kammala ta a 2007.Daga nan kuma na ci gaba da karatu a wurin Malamai, sanna kuma na yi Diploma a fannin Larabci," a cewarsa.

Abin da ya fi ba shi wahala a wajen karatun Alkur'ani

Ustaz Adam ya bayyana cewa babban abin da ya fi ba shi wahala a wajen karatun Alkur'ani shi ne "yanayin yadda zan ci na sha da kuma wurin kwanciya" yana mai cewa ko a yanzu kowa ya san irin halin da almajirai suke shiga.

Ya kara da cewa yawace-yawancen bara na cikin abubuwan da suka ba shi wahala ganin cewa kafin ya bar gidansu bai rasa abinci da abin sha ba.

Malamin ya ce babban abin farin ciki da ba zai manta da shi ba shi ne "ranar da na dira kasar Saudiyya na yi arba da Ka'abah." Sai dai ya ce babban abin da ya bata masa rai shi ne yadda aka dakatar da shi daga limanci sakamakon wasu kalamai da ya yi masu zafi game da yadda ake tafiyar da al'amuran Najeriya.

Me ya sa ake kira na 'Albanin Gombe'?

Ustaz Adam ya bayyana cewa ana kiran sa da suna Albanin Gombe ne saboda "lokacin da nake karatu akwai malaman da na tasirantu da karatunsu, amma daga cikin wadanda suka fi tasiri a rayuwata shi ne Sheikh Muhammad Awwal Albany, domin kuwa har ta kai na haddace kaset din karatunsa kamar yadda ake haddace Fatiha."

"Har ya kai nakan zauna na yi irin yadda ya karantar da wani littafi ko ya bayar da wata lacca, kamar shi ne yake gabatarwa. To, galibi idan na zo bayani nakan ce 'Malam Awwal Albany ya ce kaza, ko kuma ya bayyana kaza; to, sauran dalibai da abokaina na karatu ya suka rika kira na da Albani'. Har ta kai ga ni da wasu dalibai mun kai masa ziyara a Zaria ana saura kusan makonni uku ya rasu. A nan ne shi da kansa ya ce lallai na tabbata Albany na Gombe", in ji malamin.

Iyali

Malamin ya ce a halin yanzu yana da mata biyu da 'ya'ya goma.

Abincin da ya fi so

Ustaz Adam ya ce yana matukar son cin wake-da-shinkafa da dan wake "musamman idan aka sa masa kwai a ciki da ganye."



Read full article

Source: BBC
Related Articles: