BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Ku san malamanku tare da Sheikh Khuzaima Isma'ila Idris

 124713900 P0c6jh8g Malam Khuzaima Isma'ila Idris bin Sulaiman

Sat, 14 May 2022 Source: BBC

Iyayen Malam Khuzaima Isma'ila Idris bin Sulaiman, Ardo Abdullahi asali mutanen Jahun ne, daga bisani suka koma Jihar Bauchin Najeriya.

Amma shi Malam Khuzaima an haife shi ne a garin Jos a unguwar Dodo. Ya fara neman ilimi daga wurin mahaifinsa na addini da boko.

Ya yi karatun addini a wajen yayarsa mai suna Basma, saboda girma da rashin lafiya da ta samu mahaifinsu, wanda ya sanya ba zai iya ci gaba da koyar da su ba.

Ya samu sakafa sosai a hannun mahaifinsu da ya tarbiyyantar da su a kan cewa karatu nishadi ne, yana yawan zama da yammaci a kofar gida inda yake rera koyar da su wakokin Shehu Usman Dan Fodio cikin harshen Larabci da Filatanci.

Sun yi karatu mai zurfi na littafan addini, yayin da suka yi karatun Alkur'ani a wajen Sheikh Saleh wanda gida guda suka taso. Ita ma Kakarsu mai suna Miyangwal, ita ma sun koyi rubuta Alkur'ani da take yi, wannan ne ya ba shi damar abin da ya kira share fagen shiga makaranta.

Ya shiga fagen karatun Asasul Islamiyya, sai kuma Sanawiyya. A shekarar 2006 ya tafi makarantar koyon harshen Larabci da ke kasar Sudan, ya kwashe shekara guda yana koyo, kuma da yake yana hadawa da fannin karatun Boko ya tafi British Institution, ya yi karatun karamar Diploma a fannin Kimiyyar Kwamfuta.

Ya sake komawa Jami'ar Kuliyatul Jabra ya yi karatun Da'awa. Jami'atul Sudanil Maftuha da ke kasar Sudan da har yanzu yake karatu anan.

Sheikh Khuzaima ya yi nasarar sauke Alkur'ani mai girma, kasancewar kakarsu marubuciyar Alkurani ce ta ruwayar Warshu, Suratul Baqra na daga cikin surorun da ke birgishe kasancewar a cikinta Ayatul Kursiyyu da Amanarrasulu da Ayatul Daim suke.

Kasancewar hakan ya sanya kullum da safe sai ya karanta surar. Surar da ta fi ba shi wahalar karatu ita ce Suratul Baqra, ya kan yi tuntube sosai kafin ya samu kammalawa.

Abin da ya fi komai sanya shi nishadi, shi ne sauraren mahaifinsa idan ya na karatu ko rera wakokin Shehu Usman dan Fodio, hakan ya sanya ya ke yawan kwaikwayon yadda mahaifin na sa ke karatun.

Ranar da ya haddace Suratul Baqra ita ce rana mafi farin ciki gare shi. Ranar da mahaifinsa ya rasu ita ce mafi muni da bakin ciki a gare shi, ''Lokacin ina dawowa daga inda nake koyon kareti, ina kan hanya aka sanar dani rasuwar mahaifina, tun daga nan na shiga cikin tashin hankali da bakin ciki,'' in ji Malamin.

Tabbatar da ci gaban Sunnah na daga cikin abu mai faranta ran Malamin, take gaskiya ko kauce wa fadar ta na bakanta wa malamin rai.

Tuwon masara, da sakwara, da tuwon shinkafa na daga cikin abincin da Malamin ya fi son ya ci. Yana da mace guda daya da 'ya'ya uku.



Read full article

Source: BBC