BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Legas: Ana zargin 'yan okada da kashe babban jami'in ɗan sanda

 120715687 25f0cacf 3405 46f5 89e6 Fa9f48e2c630 Wasu yan sandan Najeriya

Tue, 28 Sep 2021 Source: BBC

Rundunar 'yan sandan jihar Legas da ke kudancin Najeriya, ta cafke mutum sittin da ake zargi da kisan wani babban jami'in ɗan sanda, CSP Kazeem Abunde, a jihar Legas.

Ana zargin 'ƴan okada masu haya da babura da ke a rukunin gidaje na Ajao Estae, da kashe ɗan sandan a yayin da ɗan sandan da tawagarsa suka kai wani samame kan kokarin hana hawa manyan hanyoyi da gadojin dake a yankunan jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Legas, Hakim Odomasu, ya bayyana mutuwar jami'in dan sandan a matsayin asara mai sosa rai.

Mr Odumaso, ya ce rundunarsu za ta tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi, inda ya kara da cewa tuni aka kama mutum sittin da ake zargi, yayin da ake ci gaba da bincike kuma.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa an kwato bindigogin da aka kwace daga hannun 'yan sandan da suka kai samamen, yayin da ake ci gaba da kula da wadanda suka samu rauni.

Wata cibiyar yaki da cin zarafin al'umma a Legas, ta ce kisan jami'in dan sandan a lokacin da yake tsaka da gudanar da aiki, barazana ce ga harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a a jihar.

Kungiyar ta shawarci gwamnan jihar ta Legas da ya dai-daita ayyukan masu babura.

A bangare guda kuma, kungiyar da ke kula da zirga-zirgar ababan hawa na babura ta ce tana gudanar da bincike, kuma hakan ya sa ta jaddada bukatar da ke da akwai na yin tankade da rairaya a cikin masu okada.

Tuni dai masu baburan suka nesanta kansu da abin da ya faru na kisan babban jami'in dan sandan.

Mutuwar CSP Kazeem Abunde, ta zo ne watanni kadan kafin ya yi riyata daga aiki, inda zai yi ritayar a watan Yunin shekarar 2022.



Read full article

Source: BBC