BBC

News

Entertainment

Sports

Business

Africa

Live Radio

Country

Webbers

Lifestyle

SIL

Liverpool 3-0 Crystal Palace: Liverpool ta yi wasa biyar a jere ba a doke ta ba

 120614285 Gettyimages 1341114605 Sadio Mane (dama) ya ci kwallo na 100 a Firimiya

Sun, 19 Sep 2021 Source: BBC

Liverpool ta yi wasa biyar a jere ba a doke ta ba a Premier League a bana, bayan da Sadio Mane ya ci kwallo na 100 a karawar da ta doke Crystal Palace.

Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta barar da damarmaki da yawa, kafin daga baya dan wasan tawagar Senegal ya ci kwallo tun kan hutu.

Mohamed Salah ne ya ci na biyu kuma na 99 da ya ci wa Liverpool a Premier, sannan na 101 da ya zura a raga a gasar har da biyun da ya ci a lokacin da ya buga wa Chelsea tamaula.

Kungiyar ta Anfield ta ci na uku ta hannun Naby Keita, kenan ta ci karawa hudu da kunnen doki 1-1 da Chelsea a gida.

Liverpool ta kara samun kwarin giwa a wasanninta, bayan da ta yi nasara a kan AC Milan da ci 3-2 ranar Laraba a Anfield a gasar Champions League.

Da wannan sakamakon na ranar Liverpool mai wasa biyar ta hau kan teburi da maki 13, yayin da Palace take ta 10 a teburin na Premier League na bana.

Bayan da Mane ya ci Palace a wasan karshe a bara da wadda ya zura a raga ranar Asabar ya zama ya ci kungiyar kwallo tara kenan.

Jumulla, Mane ya zura kwallo 13 a ragar Palace a Premier League kuma kwallo na 100 da ya ci wa Liverpool a dukkan fafatawa.

A karawar ta mako na biyar a gasar ta Premier League a bana, Wilfred Zaha dan kwallon Crystal Palace ya buga wasa na 250 a gasar.



Read full article

Source: BBC